2027: Mijin Laila, Yusuf Gagdi Ya Rasa Tikitin Komawa Majalisar Wakilai a APC

2027: Mijin Laila, Yusuf Gagdi Ya Rasa Tikitin Komawa Majalisar Wakilai a APC

  • Dan majalisar wakilai daga Plateau Yusuf Gagdi ya rasa tikitin takarar APC bayan John Tongshinen ya doke shi da gagarumin rinjayen kuri’u
  • Rahotanni sun nuna cewa John Tongshinen ya samu kuri’u 29,968 yayin da Yusuf Gagdi ya samu kuri’u 5,849 kacal a zaben fidda gwani
  • Jami’an INEC da hukumomin tsaro sun sanya ido kan zaben fidda gwanin da aka gudanar a kananan hukumomin mazabar Pankshin da Kanke da Kanam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jos, Plateau - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Pankshin da Kanke da Kanam, Yusuf Gagdi ya gaza samun tikitin APC domin komawa majalisar karo na uku.

Rahotanni sun bayyana cewa Gagdi ya sha kaye ne a hannun Dr John Tongshinen wanda ya samu rinjayen kuri’u a zaben fidda gwani na kai tsaye.

Kara karanta wannan

Yusuf Buhari ya san matsayarsa bayan kammala zaben fitar da gwani na APC a Katsina

Yusuf Gagdi ya rasa tikitin takara a APC
Dan majalisar tarayya daga Plateau, Hon. Yusuf Gagdi. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Yadda Gagdi ya rasa tikitin takarar APC

An bayyana cewa John Tongshinen ya samu kuri’u 29,968 yayin da Yusuf Gagdi wanda ke kan kujerar ya samu kuri’u 5,849 kacal a zaben, cewar Punch.

Jami’in da ya jagoranci zaben Monday Daspan ne ya sanar da sakamakon a hedkwatar mazabar da ke Pankshin ranar Lahadi bayan kammala tattara sakamako.

Daspan ya bayyana cewa an gudanar da zaben ne karkashin kulawar jami’an hukumar INEC tare da jami’an tsaro da suka sanya ido kan aikin.

Ishaya ya ce Dakta John Tongshinen ya samu ƙuri’u 29,968 inda ya doke Gagdi, abokin hamayyarsa mafi kusa, wanda ya samu ƙuri’u 5,849.

Ya ce:

“Da ikon da aka ba ni a matsayin shugaban wannan kwamitin, ina ayyana Mista John Tongshinen a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na APC na mazaɓar tarayya ta Pankshin/Kanke/Kanam.”

Ishaya ya bayyana cewa jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) sun sanya ido kan gudanar da zaɓen fidda gwanin.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a zaben fitar da gwani na APC, an tarwatsa masu kada kuri'a

Yan majalisa da dama sun rasa tikiti a APC
Taswirar jihar Plateau da Hon. Yusuf Gagdi ya fito. Hoto: Legit.
Source: Original

Kwamirin da Gagdi ke jagoranta a majalisa

Yusuf Gagdi dai shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da rundunar sojin ruwa ta Najeriya kafin rashin nasarar da ya yi.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da zaben fidda gwanin APC a dukkan kananan hukumomi uku da suka hada mazabar tarayyar da Gagdi ke wakilta.

Jam’iyyar APC ta ci gaba da gudanar da zabukan fidda gwani a jihohi daban-daban yayin da wasu ’yan majalisa ke rasa damar komawa takara a 2027.

Magoya bayan John Tongshinen sun bayyana farin cikinsu bayan sanar da nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a Plateau, cewar Vanguard.

Yusuf Buhari ya samu tikitin takarar APC

An ji cewa jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fitar da gwani a mazabar tarayya ta Sandamu/Daura/Mai'Adua a jihar Katsina.

Dan tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadi Buhari, Yusuf Buhari ya fafata da dan tsohon shugaban hukumar DSS, Auwal Lawal Musa.

Bayan kammala zaben fitar da gwanin, an sanar da Yusuf Buhari a matsayin wanda ya yi nasara inda ya ba abokin hamayyarsa tazara mai nisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com