Bayan Ganin Jinjirin Wata, Saudiyya Ta Sanar da Ranakun Hawan Arafah da Babbar Sallah

Bayan Ganin Jinjirin Wata, Saudiyya Ta Sanar da Ranakun Hawan Arafah da Babbar Sallah

  • Gwamnatin kasar Saudiyya ta ayyana gobe Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026 a matsayin ranar farko ta watan Zul Hijja na shekarar 1447 bayan hijira
  • Hakan ya biyo bayan ganin jinjirin watan a yammacin yau Laraba, 17 ga watan Mayu, 2026, wanda ya tabbatar da karewar watan Zul Ka'ada
  • Sakamakon haka, za a yi hawan Arafah a ranar Talata, 26 ga Mayu da babbar Sallah ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2026 a kasar Saudiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Kasar Saudiyya ta tabbatar da cewa an ga jinjirin watan Zul-Hijja a yau Lahadi, 29 ga watan Zul Ka'ada, 1447AH wanda ya zo daidai da 17 ga watan Mayu, 2026.

Sakamakon haka, gwamnatin Saudiyya ta ayyana gobe Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026 a matsayin 1 ga watan Zul-Hijja, wata na 12 a jerin watannin addinin musulunci.

Kara karanta wannan

Allah ya kawo mu, Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa kan ranar babbar Sallah a Najeriya

Wata.
Yadda na'ura ta hasko jinjirin wata a sararin samaniya Hoto: @Haramaininfo
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da masarautar Saudiyya ta fitar kuma aka wallafa ta a shafin hukumar kula da masallatai masu alfarma na Makkah da Madinah na manhajar X.

Ranakun Arafah da Babbar Sallah

Sanarwar ta bayyana cewa sakamakon ganin jinjirin wata, za a yi hawan Arafah a ranar Talata, 9 ga watan Zul-Hijja, 1447AH daidai da 26 ga watan Mayu, 2026.

Haka zalika Saudiyya ta ayyana ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2026 a matsayin ranar babbar Sallah (Eid el-Adha) wacce ake yi washe garin ranar Arafah, 10 ga Zul-Hijjah.

Sanarwar ta ce:

"An ga jinjirin wata na Zul Hijjah 1447 a Saudiyya. Sakamakon haka, watan Zul Hijjah mai albarka zai fara a daren yau, kuma za a yi bikin babar sallah, Eid al-Adha a ranar Laraba 27 ga Mayu 2026, in sha Allah."

Saudiyya ta yi wa alhazai fatan alheri

Saudiyya ta kuma yi wa musulman da suka je kasar aikin Hajji fatan yin ibada karbabba, tare da addu'ar Allah Ya mayar da kowanensu gida lafiya.

Kara karanta wannan

Farashin wake, doya da sauran kayan abinci ya haura sama a Kano da wasu jihohi

"Allah SWT Ya ba wa masu aikin Hajji damar kammala wannan ibada lafiya, kuma karbabba, ya sauƙaƙa musu kowane mataki na tafiyarsu, Ya kuma gafarta masu, Ya mayar da su gida kamar ranar da aka haife su.
"Muna rokon Allah Ya kuma ba mu damar dagewa a kwanaki goma na farko na Zul Hijjah wajen zikiri, azumi, addu'a, sadaka da ayyukan alheri, Ya kuma karɓi dukkan ibadunmu da ƙoƙarinmu," in ji sanarwar.
Wata.
Yadda ake duban jinjirin wata da na'urar hangen nesa a lasar Saudiyya Hoto: Inside The Haramain
Source: Facebook

Za a fara duban watan Sallah a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci daukacin al'ummar musulmin Najeriya su fita duban jinjirin watan Zul-Hijja, 1447AH.

A wata sanarwa da fadar Sarkin Musulmi ta fitar, ta ce za a fara duban watan ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Mayu, 2026 wanda ya zo daidai da 29 ga Zul Ki'ida.

Sanarwar ta bukaci duk wanda ya ga watan ya kai rahoto ga Hakimai ko dagattai mafi kusa da shi domin isar da sakon ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar CFR.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262