Trump Ya Wallafa Bidiyon Faston Najeriya da Ke Kiransa Ya Taimaki Kiristoci
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya yada wani faifan bidiyo da fasto a Najeriya ke neman taimakonsa kan zargin kisan Kiristoci
- Fasto Ezekiel Dachomo ya yi kira ga Trump da Majalisar Dinkin Duniya su taimaka wajen dakatar da abin da ya kira kisan kare dangi
- Sake wallafa bidiyon ya zo ne bayan Trump ya sanar da kashe wani babban kwamandan ISIS a hadin gwiwar sojojin Amurka da Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Wani bidiyon fasto daga jihar Plateau ya ja hankalin shugaban kasar Amurka, Donald Trump bayan watanni da wallafa shi.
Trump ya yada bidiyo da wani faston Najeriya, Ezekiel Dachomo ke kira da a taimaka wajen kare Kiristoci a kasar.

Source: Twitter
Kisan Kiristoci: Trump ya ji maganar faston Najeriya
Trump ya sake wallafa bidiyon ne a shafinsa na Truth Social bayan bidiyon ya fara yaduwa sosai a kafafen sada zumunta kusan watanni shida da suka gabata.
Bidiyon ya nuna Fasto Ezekiel Dachomo yana magana yayin jana’izar wasu Kiristoci da ya ce an kashe su a hare-haren da aka kai musu a Najeriya.
Faston ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da sanatocin Amurka da su taimaka wajen dakatar da kashe-kashen Kiristoci da ake zargin na ci gaba.
Korafin da faston ke yi ga Donald Trump
Faston ya bayyana cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya tare da zargin cewa babu wanda ke daukar mataki domin kawo karshen rikicin da ake ciki.
Sake wallafa bidiyon ya zo ne bayan Trump ya sanar da wani samame da sojojin Amurka da na Najeriya suka gudanar a kan mayakan ISIS.
Trump ya ce samamen hadin gwiwar ya yi sanadin kashe Abu-Bilal al-Minuki wanda aka bayyana a matsayin mataimakin shugaban ISIS na duniya na biyu.
Shugaban Amurkan ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne bayan tattara bayanan sirri kan ayyukan jagoran kungiyar a nahiyar Afirka baki daya.
Trump ya kara da cewa mutuwar al-Minuki za ta rage karfin kungiyar ISIS wajen gudanar da hare-hare tare da rage tasirinta a nahiyar Afirka.

Source: Facebook
Martanin gwamnatin Najeriya kan zargin kisan Kiristoci
Zargin kisan Kiristoci a Najeriya ya tayar da kura inda hankula suka tashi game da lamarin wanda ya jawo mabambantan ra'ayoyi.
Gwamnatin Najeriya a lokuta da dama ta sha musanta rahoton kisan kiyashi kan Kiristoci inda ta ce matsalar tsaro ba ruwanta da maganar addini.
Duk da haka, mutane da dama na kiran a kawo karshen matsalar tsaro da kejawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma ba tare da la'akari da addininsu ba.
Baban Chinedu ya tonawa Dachomo asiri
A baya, an ji cewa Malam Yusuf Haruna wanda aka fi sani da Baban Chinedu ya dura kan limamin addinin kirista a jihar Plateau, Fasto Ezekiel Dachomo.
Baban Chinedu ya zargi Dachomo da kasancewa tsohon ɗan fashi, da ƙirƙirar labarin haduwarsa da Yesu bayan hari a banki.
Fasto Dachomo na daga cikin Fastoci da suka yi ta korafi kan zargin kisan Kiristoci da ya ja hankalin Amurka da Donald Trump.
Asali: Legit.ng

