Babban Jami'i a Gwamnatin Bauchi Ya Rasu a Makkah ana Shirin Fara Aikin Hajji
- Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da rasuwar daya daga cikin jami'anta a kasar Saudiyya wanda ya je aikin hajji
- Marigayin wanda shi ne babban sakataren musamman a ofishin Sakataren Gwamnatin jihar ya rasu bayan jinya
- Marigayin wanda aka fi sani da Turakin Dawakin Misau ya rasu ne ana saura kwanaki kadan a fara aiki hajj a Saudiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Gwamna Bala Mohammed ya jajanta wa iyalai da abokan aikin daya daga cikin jami'an gwamnatinsa da ya rasu a Saudiyya.
Marigayin, Alhaji Shehu Yahaya Jalam shi ne babban sakatare mai kula da ayyuka na musamman a ofishin sakataren gwamnatin Bauchi.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba gwamna Bala Mohammed shawara kan yada labarai, Mukhtar Gidado ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
Bayan sun yi barazana, gwamnatin tarayya ta amince da karin alawus na 40% ga ma’aikata
Bauchi ta yi rashin mahajjaci a Saudiyya
A cikin sanarwar, gwamnatin Bauchi ta bayyana rasuwar da matukar alhini inda ta bayyana shi a matsayin mutumin kirki.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne da safiyar Lahadi bayan gajeruwar rashin lafiya yayin da yake cikin tawagar alhazan Bauchi a Saudiyya.
Marigayin wanda ke rike da sarautar Turakin Dawakin Misau ya kasance daya daga cikin jami’an gwamnati masu taimakawa wajen tsara ayyukan hajji da sauran harkokin gwamnati.
Sanarwar ta ce marigayin ma’aikaci ne mai kwazo, biyayya da sadaukarwa wanda ya bayar da rayuwarsa wajen yi wa gwamnatin Bauchi hidima tsawon shekaru.

Source: Original
Gwamna ya yi jimamin rashin da aka yi
Mukhtar Gidado ya ce rasuwar tasa babban gibi ba ga iyalansa kadai ba, har ma da gwamnati da al’ummar da suka amfana da kwarewarsa.
An gudanar da sallar jana’izarsa ne bayan sallar Azahar a masallacin Ka’aba da ke birnin Makkah ranar Lahadi bayan tabbatar da rasuwarsa.
Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan
An saki sunayen kananan hukumomi 3 da Boko Haram ta tilasta wa biyan haraji a Yobe
"Marigayi Alhaji Shehu Yahaya Jalam ya kasance jajirtacce, mai biyayya kuma ƙwararren ma’aikacin gwamnati wanda ya sadaukar da rayuwarsa da ƙarfinsa wajen yi wa Bauchi hidima.
" Ya taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukan aikin Hajji da suka gabata cikin nasara tare da sauran ayyukan gwamnati da aka ɗora masa alhaki.
"Rasuwarsa babban rashi ne ba kawai ga iyalansa da abokan aikinsa ba, har ma ga gwamnatin Bauchi baki ɗaya da sauran al’umma da suka amfana da jajircewarsa, tawali’unsa da kuma ƙwazonsa wajen aiki."
Gwamna Bala Mohammed ya mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, ofishin sakataren gwamnatin Bauchi, shugaban ma’aikata, masarautun Misau da Dambam da sauran abokan hulda.
Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta kura-kuransa, ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus tare da bai wa iyalansa hakurin jure rashin.
Mahaukaciya ta rasu a kasar Saudiyya
Mun ba ku labarin cewa wata maniyyaciya ƴar shekara 73 daga Jihar Adamawa, Mallama Aishatu Muhammadu, ta rasu a hanyarta ta zuwa Madina.
Hukumar NAHCON ta bayyana cewa ciwon zuciya ne ya yi sanadin mutuwar tata yayin da take cikin tafiya daga birnin Jeddah.
Shugaban NAHCON ya jajanta wa iyalan mamaciyar tare da ba su tabbacin dawo masu da dukkan kayayyakin da ta bari a ƙasa mai tsarki.
Asali: Legit.ng