"A Rama Biki": Sanata Yari Ya ba 'Yan Arewa Shawara kan Tazarcen Tinubu a 2027

"A Rama Biki": Sanata Yari Ya ba 'Yan Arewa Shawara kan Tazarcen Tinubu a 2027

  • Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar dattawa,.Abdulaziz Yari, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Abdulaziz Yari ya tuna da irin goyon bayan da yankin Kudu maso Yamma ya bayar ga marigayi Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023
  • Sanatan ya bukaci 'yan Arewa da su rama biki wajen sake zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 da ke tafe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya buƙaci ’yan Arewa da su marawa sake zaɓen Bola Tinubu baya a shekarar 2027.

Sanata Abdulazizi Yari ya jaddada cewa ya kamata a ƙyale Kudancin Najeriya su kammala wa’adinsu na shekaru takwas domin muradin haɗin kan ƙasa da daidaiton siyasa.

Yari ya bukaci Areqa ta sake zaben Tinubu a 2027
Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari Hoto: Almansoor Gusau
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce Yari ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar, 16 ga watan Mayun 2026 yayin wani taro da ya yi da malaman addinin Musulunci a Talata-Mafara.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa ya yi wa 'yan Arewa barazana kan zaben 2027? Gaskiya ta fito

Abdulaziz Yari ya bukaci a yi addua

Abdulaziz Yari ya kuma buƙaci shugabannin addinin da su tsananta addu’o’i domin samun dorewar zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar.

Sanatan, wanda ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar dattawa, ya ce dole ne yankin a yanzu ya “saka wa” goyon bayan da aka ba wa Buhari tsakanin shekarar 2015 da 2023.

Yari ya tuna baya kan kawancen Arewa da Kudu

Ya jaddada cewa kawance tsakanin Arewacin Najeriya da Kudu maso Yamma ya kasance mai matuƙar muhimmanci ga siyasar ƙasa da kuma nasarar zaɓe.

Yayin da yake magana kan buƙatar haɗin kan siyasa gabannin kakar zaɓe ta gaba, tsohon gwamnan ya siffanta alaƙar dake tsakanin yankunan biyu a matsayin dabarar da ta daɗe da kafuwa wadda ya kamata a dore da ita.

“Zaɓe yana kusa, kuma wannan shi ne lokacin da muke buƙatar addu’o’i, kuma wannan haɗin gwiwa tsakanin Arewacin Najeriya da Kudu maso Yamma wani abu ne da Kudu maso Yamma ta riga ta sauke nata nauyin tsakanin 2015 da 2023."

Kara karanta wannan

An dora Hayatu Deen a gaban Atiku, Obi da Amaechi a takarar zama shugaban kasa a 2027

- Sanata Abdulaziz Yari

Yari ya bukaci a sake zaben Tinubu a 2027
Sanata Abdulaziz Yari na jawabi a wajen taro Hoto: Almansoor Gusau
Source: Facebook

Yari ya bukaci a zabi Tinubu a 2027

A cewarsa, Kudu maso Yamma ta tsaya tsayin daka a bayan Buhari a duk tsawon lokacin shugabancinsa, hakan ya sa ya zama dole ga yankin Arewa maso Yamma su rama wannan karramawa ta hanyar marawa burin sake zaɓen Tinubu baya.

“Saboda haka mu a wannan ɓangare na ƙasa, musamman mu a Arewa maso Yamma, ba mu da wani dalili bayan da Bola Tinubu da Kudu maso Yamma suka ba Muhammadu Buhari dukkan goyon baya tsakanin 2015 zuwa 2019 da kuma 2019 zuwa 2023 ga nasararsa da kuma shugabancinsa.”
“Ina ganin a gare mu, lokaci ya yi da za mu saka musu."

- Sanata Abdulaziz Yari

Abdulaziz Yari ya gana da Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi wata ganawa da Sanata Abdulaziz Yari.

Majiyoyi sun bayyana cewa an gudanar da taron ne ta bayan fage, inda babu wani daga cikin bangarorin biyu da ya fito ya yi wa manema labarai bayani.

Sanata Abdulaziz Yari da ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar dattawa ya gana da Atiku ne a gidan tsohon mataimakin shugaban kasar da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng