NNPP, NDC Sun Fara Zazzafar Musayar Yawu game da Takarar Obi da Kwankwaso
- NNPP ta ce tsofaffin shugabanninta sun yi ƙoƙarin haɗa jam'iyyar da NDC domin goyon bayan Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a zaɓen 2027
- Sai dai jam'iyyar adawa ta NDC ta musanta zargin, tana mai cewa ba ta da wata yarjejeniya ko shirin haɗaka da NNPP kan batun takarar
- Yanzu haka, dukkannin bangarorin biyu sun ci gaba da musayar zarge-zarge kan rade-radin haɗakar siyasa kafin babban zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam'iyyar NNPP da NDC sun shiga musayar kalamai kan wani zargi da ke cewa ana shirin haɗa tsohuwar jam'iyyar Kwankwaso da gamayyar jam'iyyun adawa domin mara wa tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso baya.
Sabuwar takaddamar ta biyo bayan ci gaba da yaɗuwar rade-radin cewa ana tattaunawar kafa haɗaka tsakanin Obi da Kwankwaso, zargin da NNPP ta sha musantawa.

Source: Twitter
Kafar Arise ta kawo labarin cewa shugaban NNPP na ƙasa, Major Agbo, ya zargi tsofaffin shugabannin jam'iyyar da ƙoƙarin haɗa tsarin NNPP a cikin abin da ya kira "tsarin Obi da Kwankwaso" a ƙarƙashin NDC.
NNPP ta yi magana kan Obi/Kwankwaso
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa, tsohon shugaban jam'iyyar na ƙasa, Bala Yusuf, da tawagarsa sun shirya narkar da jam'iyyar domin goyon bayan Kwankwaso kafin sababbin shugabanni su karɓi ragamar jagoranci.
Agbo ya ce:
"Ya yi ƙarya. Da a ce sun ci gaba, da sun narkar da dukkkannin tsarin jam'iyyar cikin shirin shugaban nasu. Wannan shi ne irin kwaɗayin da ke tattare da su."
Ya kuma jaddada cewa matakin da NNPP ta ɗauka na tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa na wucin gadi domin cika wa'adin hukumar zaɓe ne kawai, ba alamar wata haɗaka da NDC ko APC ba ce.
Martanin NDC ga NNPP
Da yake mayar da martani, mataimakin sakataren yaɗa labarai na ƙasa na NDC, Abdulmumin Abdulsalam, ya yi watsi da zargin, yana mai cewa jam'iyyarsa ba ta da wata yarjejeniya ko shirin siyasa da NNPP.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su

Source: Facebook
Ya ce:
"Ba mu da wata yarjejeniya da NNPP ko wata jam'iyya, musamman a siyasar Kano. NDC jirgin ƙasa ne da ke tafiya, kuma irin ƙarfinta a yanzu ya ishe ta."
Abdulsalam ya ƙara da cewa, ganin yadda NNPP ta rasa fitattun mambobinta da dama, ita ce za ta fi neman haɗaka domin samun sabon ƙarfi a siyasa, ba NDC ba.
An gano wanda ya hada Obi da Kwankwaso
A baya, kun samu labarin cewa kungiyar Yoruba Ronu ta hakikance cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya hada tikitin takarar Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi.
An yi zargin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da yi wa Bola Tinubu aiki a boye domin tazarce a 2027 ta hanyar hada 'yan takarar NDC da ke kokarin lallai sai an kayar da Bola Tinubu.
Tsohon mai ba Obasanjo shawara kan harkokin siyasa, Dakta Akin Osuntokun, ya yi magana kan ikirarin cewa Obasanjo ne ya hada tikitin Peter Obi da Kwankwaso amma da zummar taimakon Tinubu ba.
Asali: Legit.ng
