Hukumar Tace Fina Finai Ta Dakatar da Jarumai 2 kan Tallata Fim Din 'Abadan'
- Hukumar tace fina-finai ta Kano ta dakatar da Amina Uba Hassan da Adam Garba da ake kira Raba Gardama
- Majiyoyi suka ce an dakatar da jaruman ne guda biyu daga harkokin Kannywood na shekara guda saboda wani bidiyo
- Hukumar ta bayyana cewa bidiyon ya tayar da kura a Kano, tare da zargin cewa ya saɓa da tarbiyya da ƙa’idodin masana’antar shirya fina-finai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba El-Mustapha ya gargadi jarumai, masu shirya fim da daraktoci kan shirya fina-finai.
El-Mustapha ya bukaci su mutunta dokokin hukumar domin kare mutuncin masana’antar Kannywood bayan dakatar da wasu jarumai biyu.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya wallafa ranar Lahadi 17 ga watan Mayun shekarar 2026, cewar Freedom Radio.
Musabbabin dakatar da jaruman 2 a Kannywood
Abdullahi Sani Sulaiman ya ce matakin ya biyo bayan abin da hukumar ta gani a matsayin rashin da'a musamman tallar fim din wanda ya saba da al'adar Hausawa da Musulmi.
Hukumar tace fina-finai ta haramta shahararrun jaruman Kannywood biyu ci gaba da aiki a masana’antar na tsawon shekara guda.
Jaruman da abin ya shafa sun haɗa da Amina Uba Hassan da Adam Garba, wanda aka fi sani da Raba Gardama, bayan wata takaddama ta bidiyon tallar fim din.
Sanarwar ta ce hukumar ta ɗauki wannan hukunci ne domin tabbatar da da’a da kuma kiyaye ƙa’idojin da ke tafiyar da harkokin Kannywood a Kano.
Hukumar ta jaddada cewa dokarta ta ba ta damar hukunta duk wani ɗan fim da aka samu da karya ƙa’idoji ko aikata abin da bai dace ba.
Ta kuma yi gargadin cewa duk wanda ya karya umarnin dakatarwar zai iya fuskantar tsauraran matakan hukunci kamar yadda doka ta tanada a jihar Kano.

Kara karanta wannan
Kotu ta yanke wa Halima Umar hukunci bayan kama ta da makamai masu hadari a Filato

Source: Facebook
Shugaban hukumar Abba El-Mustapha ya shawarci jarumai da sauran masu ruwa da tsaki su guji abubuwan da za su zubar da kimar Kannywood.
Haka kuma hukumar ta umarci producers da directors su bi umarnin dakatarwar, tana mai cewa yin watsi da matakin tamkar raina ikon hukumar ce.
Fitar da tallar fim din dai ya jawo maganganu inda mutane da dama ke ganin bai dace a yi tallarsa ba ma bare a har a kai ga sake shi.
Ce-ce-ku-cen ya jawo hankalin hukumar da kuma masu ruwa da tsaki da suke ganin ya dace su dauki matakin da ya dace.
2027: Mansurah Isa ta shirya tallata Tinubu
Kun ji cewa yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, 'yan siyasa na cigaba da bayyana manufosinsu domin samun goyon bayan jama'ar kasar nan.
Jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta bayyana cewa za ta yi mai yiwuwa wajen tallata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Mansurah Isah ta sanar da cewa ita asalin 'yar jam'iyyar APC ce a Najeriya, inda ta ce ta shafe sama da shekara 10 tana tafiyar siyasar.
Asali: Legit.ng
