Yadda Sojojin Amurka da Najeriya Suka Fafata da 'Yan Ta'adda wajen Kashe Al Minuki

Yadda Sojojin Amurka da Najeriya Suka Fafata da 'Yan Ta'adda wajen Kashe Al Minuki

  • Dakarun sojojin Amurka da na Najeriya sun fafata da 'yan ta'addan kungiyar ISIS a yankin Tafkin Chadi bayan sun kai hare-hare
  • Majiyoyi sun bayyana yadda aka kai hare-haren wadanda suka yi nasarar kashe babban dan ta'adda Abu-Bilal Al-Minuki da mayaka da dama
  • An bayar da tabbacin cewa ba a samu asarar rayuka ko rauni ba daga bangaren sojojin Amurka da Najeriya wadanda suka gudanar da aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Sojojin Amurka da takororinsu na Najeriya sun samu nasarar hallaka babban mataimakin shugaban kungiyar ISIS, Abu-Bilal Al-Minuki.

Sojojin sun yi musayar wuta da ’yan ta’addan ISIS na tsawon fiye da sa’o’i uku kafin su yi nasarar kashe Abu-Bilal Al-Minuki.

Sojojin Amurka da Najeriya sun kashe Al-Minuki
Dakarun sojojin Amurka a cikin jirgi Hoto: @uscentcom
Source: Twitter

Jaridar New York Times ce ta kawo rahoton musayar wutar da sojojin suka yi da mayakan kungiyar ISIS.

Kara karanta wannan

Jerin masu neman takarar majalisar tarayya da APC ta yi watsi da su a wurin tantancewa

Trump ya ce an kashe Al-Minuki

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da mutuwar Al-Minuki, kuma Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da hakan a safiyar ranar Asabar, 16 ga watan Mayun 2026.

Trump ya ce an kashe Al-Minuki ne a wani “gagarumin aiki” da dakarun Najeriya da na Amurka suka gudanar.

Yadda aka kashe Abu-Bilal Al-Minuki

An kashe Al-Minuki ne a wani hari na amfani da jirgi mai saukar ungulu da aka kai ta hanyar amfani da kwamandoji na musamman na Najeriya da Amurka kusan guda 24 waɗanda suka haɗa da mambobin rundunar Amurka ta Navy SEAL Team 6.

Yayin da take ambato jami’an Amurka guda uku, jaridar ta ce dakarun sun kai wa Al-Minuki hari ne tare da mayaka da dama kan wasu ƙananan tsibirai guda biyu a Tafkin Chadi.

Jami’an sun bayyana cewa da farko sojojin Amurka sun yi ƙoƙarin kama Al-Minuki ne da rai, amma sai suka kashe shi ta hanyar harin jirgin sama lokacin da ya bayyana sarari cewa ba zai miƙa wuya ba, maimakon su fuskanci haɗarin barinsa ya tsere.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana bayan Amurka ta yi ikirarin kashe kasurgumin dan ta'adda a Najeriya

Sojojin Amurka da Najeriya sun yi aiki tare

An bayyana cewa hare-haren da sojojin Amurka da Najeriya sun farmaki maboyarsa ne da ke yankin Tafkin Chadi.

Sun ƙara da cewa a halin yanzu masana suna bincikar wayoyin salula, kwamfutoci, da sauran bayanan na’urorin da aka samo daga wannan aiki domin samun bayanai kan ɗaukar ma’aikata, gudanar da ayyuka, da kuma hanyoyin kuɗi na rassan ISIS a Afirka da ma sauran wurare na duniya.

Sojojin Najeriya da Amurka sun kashe babban dan ta'adda a Borno
Sojojin Najeriya a bakin daga Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Ba a samu rahoton asara rai ko rauni ba a ɓangaren sojojin Amurka ko na Najeriya wadanda suka kai farmakin.

A cewar jaridar, dukkan jami’an sun yi magana ne bisa sharaɗin kada a bayyana sunayensu domin tattauna batutuwan da suka shafi gudanar da aikin sojoji.

Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ragargazar 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar karkashe ’yan tada ƙayar baya da dama, ciki har da manyan kwamandoji biyu.

Harin ya farmaki wasu muhimman wurare na ’yan ta’adda da kuma kayayyakin aikinsu a cikin maɓoyar su da ke yankin Bulabulin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng