'Yan Ta'adda Sun Hallaka Jami'an 'Yan Sanda da Dama a Yobe

'Yan Ta'adda Sun Hallaka Jami'an 'Yan Sanda da Dama a Yobe

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta rasa wasu daga cikin jami'anta sakamakon harin 'yan ta'adda da aka kai a jihar Yobe
  • 'Yan ta'addan sun kai harin ne a wata makarantar runduna ta musamman ta sojojin Najeriya inda ake ba wasu 'yan sanda horo
  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu ta bayyana cewa ba za a manta da sadaukarwar da suka yi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Yobe - Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’ai 17 biyo bayan wani harin ta’addanci da aka kai a jihar Yobe.

'Yan ta'addan sun kai harin ne a makarantar runduna ta musamman ta sojojin Najeriya da ke Buni Yadi, a karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

An kashe 'yan sanda a jihar Yobe
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DCP Anthony Placid, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X a ranar Asabar, 16 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Shirin ISWAP ya rushe, bam ya hallaka Abu Umar da wasu manyan yan ta'adda 5 a Borno

'Yan ta'adda sun kashe 'yan sanda

An ruwaito cewa jami’an suna wani babban horo na musamman kan gudanar da aiki a makarantar lokacin da ’yan ta’adda suka kai wani hari da sassafe ranar 8 ga watan Mayu, 2026.

A cewar sanarwar, maharan sun far wa rukunin horon ne ta fuskoki daban-daban da misalin ƙarfe 1:15 na dare, lamarin da ya kai ga fafatawa mai tsanani wadda a lokacin ne jami’an suka rasa rayukansu.

Haka zalika, ’yan sandan sun bayyana cewa an kashe jami’an sojojin Najeriya da dama lokacin da suke fafatawa da maharan.

Shugaban 'yan sanda ya yi ta'aziyya

Shugaban ’yan sanda na kasa, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana jami’an da aka kashe a matsayin jajirtattu kuma masu sadaukarwa waɗanda suka nuna kishin ƙasa na ban mamaki da kuma sadaukarwa ga tsaron ƙasa ta hanyar shiga cikin shirye-shiryen horon yaƙi da ta’addanci da dabarun aiki.

Ya mika ta’aziyyar rundunar ’yan sandan Najeriya ga iyalan jami’an da suka rasu, tare da ba su tabbacin cewa ba za a manta da sadaukarwar da jami’an da suka faɗi suka yi ba.

Kara karanta wannan

Lamari ya baci: 'Yan ta'addan Boko Haram sun sace dalibai da dama a Borno

A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin nuna haɗin kai, kwamishinan ’yan sanda na jihar Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin, ya ziyarci makarantar a madadin shugaban 'yan sandan Najeriya.

'Yan ta'adda sun kashe 'yan sanda a Yobe
Olatunji Rilwan Disu, shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An jajantawa sojoji

Yayin ziyarar, ya jajanta wa kwamandan makarantar, Birgediya Janar A.C. Enuagu, jami’an sojojin Najeriya, da kuma jami’an ’yan sanda da ke fuskantar horo.

Ya kuma yabi juriya da jajircewar jami’an da suka tsira, sannan ya buƙace su da su ci gaba da kasancewa masu sadaukarwa wajen kammala shirin horon domin karrama abokan aikinsu da suka rasu.

'Yan sanda sun cafke jagoran 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an 'yan sanda a jihar Zmafara sun sami nasarar cafke wani kasurgumin jagoran 'yan bindiga.

Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa ta cafke wani da ake zargi jagoran 'yan bindiga ne tare da ƙwato makamai da miyagun ƙwayoyi.

An kama wani da ake zargi jagoran 'yan bindiga ne, Audu Maikano, yayin wani samame na haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro a ƙauyen Dan-Makulu, da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng