Latest
Matafiya sun makale a Mokwa bayan mazauna Niger sun toshe hanyar Mokwa-Bida, suna zanga-zangar nuna adawa da yawaitar garkuwa da mutane da ’yan bindiga.
A labarin nan, za a ji cewa kasar Amurka ta fitar da daftarin sulhu a Gaza mai dokoki 15, amma Isra'ila ta ce sai dai bayan ran ta ne za a samar da ƙasar Falasdinu.
Bincike ya karyata ikirarin cewa an kashe shugaban karamar hukumar Bungudu, Nura Abdullahi, tana mai cewa babu sahihiyar hujjar mutuwarsa bayan garkuwa da shi.
Ambaliyar ruwa ta lalata kadarori da darajarsu ta kai miliyoyin Naira tare da mamaye gidaje a General M.I. Wushishi Housing Estate da ke Minna, Jihar Neja.
Kungiyar Idoma da ke Amurka ta shirya kai ƙorafi ga Donald Trump kan kashe-kashe da matsalar tsaro a Benue, tare da neman ƙarin tallafin ƙasa da ƙasa.
Ɗan takarar APGA a zaɓen gwamnan Osun, Adesina Adeyemi-Doro, ya janye daga takarar tare da goyi bayan ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, gabanin zaɓen 15 ga Agusta.
Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya ce Iran ta sanar da Amurka cewa ba ta da wani shiri na sanya kudin fito kan jiragen ruwa da ke amfani da mashigar Hormuz.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana waɗanda suka taimaka aka samu nasarar kammala auren gata da aka kashe N1.5bn a jihar Kano.
Jam'iyyar PDP a jihar Kebbi ta musanta rahoton goyon bayan Gwamna Nasir Idris ko APC a 2027, tana mai cewa jam’iyyar tana nan ɗaya kuma mai zaman kanta.
Masu zafi
Samu kari