Tinubu ko Atiku: An Yi Hasashen Wanda zai Lashe Zaben 2027 daga Turai

Tinubu ko Atiku: An Yi Hasashen Wanda zai Lashe Zaben 2027 daga Turai

  • Mujallar The Economist ta ce Shugaba Bola Tinubu na iya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 duk da karuwar rashin gamsuwar jama’a kan tsaro da tattalin arziki
  • Mujallar ta danganta wannan yiwuwar da tsarin siyasar Najeriya, fa’idar kasancewar Tinubu kan kujerar shugaban ƙasa da kuma rarrabuwar jam’iyyun adawa
  • Sai dai ADC da NDC sun ƙalubalanci wannan hasashe, inda suka ce matsin tattalin arziki da halin da jama’a ke ciki na iya yin tasiri sosai kan yadda za a kaɗa kuri’u

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Mujallar The Economist ta yi nazari kan zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya sake samun nasara duk da korafe-korafen da ake yi kan tsaro da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

'Babban abin da zai raba Bola Tinubu da mulkin Najeriya a 2027'

Mujallar ta ce rashin gamsuwar jama’a da gwamnatin Tinubu ba lallai ya zama dalilin da zai hana shi sake samun mulki ba, saboda wasu abubuwa da suka shafi tsarin siyasar Najeriya.

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Atiku Abubakar a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Atiku Abubakar|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Me zai iya taimakon Tinubu?

The Economist ta ce Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro da tattalin arziki, amma ta bayyana cewa fa’idar kasancewa a kan mulki da tsarin jam’iyyar APC na iya taka rawa a zaɓen.

Ta kuma yi nuni da rarrabuwar jam’iyyun adawa, inda tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar na ADC da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi na NDC, ba su takara tare.

Mujallar ta ambaci cewa hakan na iya hana kuri’un masu adawa da APC taruwa a bayan ɗan takara guda.

Ta kuma yi nuni da tasirin addini da kuma ƙarancin yawan masu kada ƙuri’a a wasu yankuna a matsayin wasu daga cikin abubuwan da za su iya shafar sakamakon zaɓen.

Matsin tattalin arziki da tsaro

The Economist ta yi amfani da Jihar Borno a matsayin misali wajen bayyana matsalolin tsaro da tattalin arziki da wasu yankuna ke fuskanta.

Ta ce hare-haren ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, garkuwa da mutane da kwace dukiyoyi sun yi illa ga tattalin arzikin yankin, tare da rage ayyukan yi da kasuwanci.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Faɗi dalilin da Ya Sa Tinubu ke Son Komawa Ƙarfi da Yaji

Mujallar ta kuma ce sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu, musamman cire tallafin man fetur, sun samu yabo daga masu zuba jari, amma ba su kai ga sauƙaƙa rayuwa ga mafi yawan ’yan Najeriya ba.

Ta ce hauhawar farashin kaya ta kasance kusan kashi 15 cikin 100 a watan Agusta, yayin da hauhawar farashin abinci ta kusan kai kashi 20 cikin 100, bisa bayanan da ta ambata.

Martanin ADC da NDC

A gefe guda, ADC ta ce ta amince da wani ɓangare na rahoton The Economist da ya bayyana cewa Tinubu ba ya samun karɓuwa sosai a tsakanin jama’a, amma ta ƙalubalanci ra’ayin cewa hakan zai ba shi damar sake lashe zaɓe.

NDC ma ta yi watsi da hasashen mujallar, inda ta tambayi dalilin da ya sa aka kai ga wannan matsaya kan yiwuwar Tinubu ci gaba da mulki.

Peter Obi na NDC
Dan takarar NDC, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Arise News ta wallafa cewa jam’iyyar ta ce ba ta ga wata hanyar da Tinubu zai sake samun mulki ba tare da magudi a tsarin zaɓe ba.

Shugaban APC ya gargadi jama'a

A wani labarin, kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC na Jihar Edo, Jarret Tenebe, ya yi magana kan shirin jam’iyyar na samar wa Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u miliyan 2.5 daga jihar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya fusata mutanen Tinubu, sun yi masa raddi mai zafi

Tenebe ya yi wannan magana ne a Benin City yayin wani taron magoya bayan jam’iyyar, inda ya yi barazanar amfani da kalaman da suka shafi bindigar AK-47 ga masu ƙoƙarin kawo cikas ga shirin samun ƙuri’un.

A cewar rahoton, Tenebe ya ce Gwamna Monday Okpebholo ya yi alkawarin samar da ƙuri’u miliyan 2.5 ga Tinubu daga Edo, yana mai cewa jam’iyyar za ta yi aiki domin cimma wannan buri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng