Lallai Tinubu Ya Sha da Ƙyar, An Gano Manhajoji 2 da Aka Yi Amfani da Su a Shirin Juyin Mulki

Lallai Tinubu Ya Sha da Ƙyar, An Gano Manhajoji 2 da Aka Yi Amfani da Su a Shirin Juyin Mulki

  • Masu bincike kan zargin yunkurin hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun gano manhajojin da aka yi amfani da su
  • Rahoto ya nuna cewa wasu da ake zargi da hannu a shirin juyin mulkin 2025 sun yi amfani da WhatsApp da Zangi wajen sadarwa
  • Kanal Mohammed Ma’aji ne ya gabatar da Zangi ga wasu daga cikin mutanen da ake bincike a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hanyar sadarwar da ake amfani da ita wajen shirya wani shiri na sirri na iya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar shirin.

A binciken zargin juyin mulkin da ake yi wa wasu jami’an soja da fararen hula, masu bincike sun gano cewa sadarwar wasu daga cikin wadanda ake zargin ba ta tsaya kan kiran waya na yau da kullum ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, an kashe fiye da 65 yayin da aka ceto mutane 360

Kanal Ma'aji.
Jagoran wadanda ake zargi da shirin juyin mulki a Najeriya, Kanal Mohammed Ma'aji Hoto: Nigerian stories
Source: Twitter

Bayanan bincike da Premium Times ta samu ta bayan fage sun nuna cewa an yi amfani da WhatsApp, yayin da tattaunawa da dama ta koma manhajar Zangi, wadda aka fi saninta da samar da hanyar sadarwa mai kare sirrin masu amfani ita.

Kanal Ma’aji ya gabatar da Zangi

Wani tsohon Kyaftin din Rundunar Sojin Ruwa, Erasmus Victor, wanda ake tuhuma tare da wasu mutane biyar kan tuhume-tuhume 13 da suka hada da cin amanar kasa, ya ba masu bincike bayani kan yadda aka yi amfani da manhajar Zangi.

A cikin bayaninsa yayin da masu binciken soji ke yi masa tambayoyi, Victor ya ce Kanal Mohammed Ma’aji, wanda ake zargi da jagorantar shirin juyin mulkin, ne ya gabatar masa da Zangi.

A cewarsa, Ma’aji ya dauki manhajar a matsayin hanyar sadarwa mafi tsaro fiye da kiran waya na yau da kullum.

Victor ya ce ya sauke manhajar ne musamman domin sadarwa da Ma’aji da kuma Shamsuddeen Bappah, wani Laftanar Kanal mai aiki a Rundunar Sojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan TikTok 3 sun fara ganin sakamako bayan sun taɓa mutuncin shugaban ƙasa

Dalilin da ya sa manhajar ta ja hankali

Zangi ta bambanta da WhatsApp saboda ba lallai sai an yi amfani da lambar wayar salula wajen yin rajista ba. Maimakon haka, mai amfani yana samun wata lambar Zangi ta musamman.

Haka kuma, kamfanin ya bayyana cewa ana kunna tsarin end-to-end encryption kai tsaye, wanda ke sa ba a iya ganin abubuwan da mutane suka tattauna a manhajar.

Duk da haka, amfani da Zangi ba yana nufin cewa tattaunawa ta zama ba za a iya bincikarta ba. A tsarin da kamfanin ya bayyana, na’urar da aka yi amfani da ita na iya zama muhimmin bangare wajen gano bayanan sadarwar.

Zangi.
Manhajar sadarwa ta zamani, Zangi Hoto: SOPA Images
Source: Getty Images

Binciken da aka gudanar kan zargin shirin kifar da gwamnatin Tinubu ya yi amfani da irin wadannan bayanan sadarwa a kokarin gano yadda wadanda ake zargi suka tsara shirinsu da kuma irin rawar da kowane mutum ya taka.

Victor ya ce bai dauki zargin shirin juyin mulkin da muhimmanci ba a lokacin, kuma daga baya ya yi nadamar rashin kai rahoton abin da ya sani ga hukumomi.

Kara karanta wannan

Bincike kan shirin yi wa Tinubu juyin mulki ya rutsa da fitaccen jarumin fim a Najeriya

Bincike ya rutsa da jarumin Nollywood

A wani labarin, kun ji cewa an zargi fitaccen jarumin Nollywood, Stanley Amandi, da amincewa da aikin shirya farfaganda domin tallafa wa wadanda suka shirya juyin mulki.

Masu bincike kan lamarin sun tatsi bayanai daga jarumin kan abin da ya shafi zargin shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262