Dan Siyasa a Kano Ya Kira Ruwa bayan Nuna Bindiga a Wurin Taro
- ’Yan sandan Kano sun gayyaci ɗan siyasa Aminu Abdullahi Warkal domin yi masa tambayoyi kan wani bidiyo da ake zargin ya nuna bindiga
- Rundunar ta ce idan aka tabbatar da zargin, nuna bindigar na iya zama saɓa wa dokar mallakar da amfani da makamai ta Najeriya
- ’Yan sanda sun gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu su guji tashin hankali tare da bin dokokin zabe da na makamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gayyaci wani ɗan siyasa, Hon. Aminu Abdullahi Warkal, domin yi masa tambayoyi kan zargin nuna bindiga ba bisa ka’ida ba a wani taron siyasa.
Rundunar ta ce ta gano wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta yayin da take gudanar da sintirin sa ido a kafafen intanet.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Litinin, 5 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
A cewar ’yan sandan, ana zargin Warkal da bayyana a cikin bidiyon yana nuna wata bindiga a wurin taro.
'Yan sandan sun ce idan aka tabbatar da zargin, lamarin na iya zama saɓa wa tanade-tanaden dokar makamai.
’Yan sanda sun koka kan nuna bindiga
Rundunar ta ce irin wannan hali na iya “tayar da tsoro, tsoratar da jama’a da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron al’umma.”
Sanarwar ta ce Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin a gayyaci Warkal zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai domin yi masa tambayoyi.
“Bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, SFIPMA, MNIM, MNIPS, MASIS, an gayyaci Hon. Aminu Abdullahi Warkal zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano,” in ji sanarwar.

Kara karanta wannan
Gwamna Zulum ya umarci cafke 'yan 'Tinubu Must Go a Borno'? An ji yadda zancen yake
Ana ci gaba da bincike kan lamarin
Rundunar ta ƙara da cewa Warkal yana hannun sashen leƙen asiri na rundunar, State Intelligence Department (SID), inda ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Sai dai ’yan sandan ba su bayyana ko an kwato bindigar da ake zargin an nuna a bidiyon ba, ko kuma Warkal ya bayar da wani bayani kan dalilin mallakarta ko nuna ta ba.
’Yan sanda sun yi gargadi kan nuna makamai
Rundunar ta yi gargadin cewa ba za ta amince da ayyukan rashin bin doka, daba da kuma nuna makaman da za su iya yin barazana ga zaman lafiyar jama’a ba, ba tare da la’akari da matsayin wanda abin ya shafa ba.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce rundunar ba za ta lamunci "duk wani aikin rashin bin doka, daba ko nuna makaman da za su iya yin barazana ga zaman lafiyar jama’a ba, ba tare da la’akari da matsayin mutumin da abin ya shafa ba.”

Source: Original
An nemi a sasanta rikicin APC a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Aminu Shehu Uba Sharada, ya nemi a yi zama domin sasanta jiga-jigan jam'iyya mai mulki.
Ya roki Shugaba Bola Tinubu da Sanata Abdulaziz Yari su hada shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kano domin sasanta bambance-bambancen da ke tsakaninsu.
Asali: Legit.ng

