‘Babban Bala’in da Ka Iya Tunkarar Najeriya idan Atiku Ya Ci Zabe a 2027’
- Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya ce zai iya goyon bayan Bola Ahmed Tinubu a takarar shekarar 2027
- Babachir ya ce kwarewarsa ta aiki da Atiku ta sauya ra’ayinsa, yana zarginsa da sauya tunani bayan tuntubar wasu mutane
- Ya kuma bayyana cewa Atiku ya taba neman ya lallashi Peter Obi ya zama abokin takararsa, amma sai ya ki amincewa da tsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, ya ce zai fi son goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a maimakon Atiku Abubakar.
Babachir Lawal ya bayyana cewa idan Najeriya ta samu matsala karkashin Tinubu, matsalar na iya kasancewa cikin tsari, amma karkashin Atiku za ta iya zama cikin rudani.

Source: Facebook
Ya yi wannan magana ne yayin wata hira da shiri da Vanguard ta bibiya inda yake bayyana dalilin adawarsa da takarar Atiku a 2027.
Sanin da Babachir ya yi wa Atiku
Lawal ya ce kwarewarsa ta baya wajen aiki da Atiku ce ta taimaka wajen sauya ra’ayinsa kan goyon bayan tsohon mataimakin shugaban.
Ya bayyana cewa a baya ya yi tunanin tallafa wa Atiku saboda yadda yake ganin halin da yankin Arewa ke ciki yana kara muni.
Lawal ya ce ya yi imanin cewa Arewa bai kamata ta mika mulkin shugaban kasa ba, domin a kalla dan yankin zai iya dakile koma bayan da ake fuskanta.
Sai dai ya ce abubuwan da ya gani lokacin da yake aiki da Atiku sun sauya ra’ayinsa, musamman yadda yake zargin sauya umarni.
A cewarsa, Atiku kan ba mutum umarni ya aiwatar, sannan daga baya ya sauya matsayar bayan tuntubar wasu mutane.
Babachir ya ce wannan dabi’a ce ta haifar da rudani a duk wani aiki da ake yi tare da tsohon mataimakin shugaban.
Ya ce rashin jituwar da ake samu kan wasu nade-naden siyasa ma ta taimaka wajen kara dagula al’amura a lokacin da suke aiki tare.

Kara karanta wannan
"Yan Najeriya ba su cancanci haka ba," Atiku ya sake aika sako mai ɗaga hankali ga Tinubu

Source: Getty Images
'Yadda Atiku ya taba rokon Peter Obi'
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya kuma bayyana cewa Atiku ya taba neman ya lallashi tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi, ya zama abokin takararsa.
A cewar Lawal, Atiku ya gabatar da shawarar cewa zai yi wa’adi guda na shekaru hudu kafin a nemi sauya kundin tsarin mulki.
Ya ce Atiku ya kuma yi shawarar mayar da wa’adin shugaban kasa zuwa wa’adi guda na shekaru shida a nan gaba.
Babachir ya bayyana cewa Atiku ya kuma yi nuni da cewa tsarin karbar shugabancin kasa zai koma yankin Kudu maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.
Ya ce saboda alakarsa da Peter Obi, ya tuntube shi domin ya amince da zama abokin takarar Atiku a zaben 2027.
Sai dai Lawal ya ce Obi ya ki amincewa da tayin, saboda wani bincike da ya yi ya nuna cewa tikitin ba zai samu nasara ba.
A cewar Lawal, Obi ya nuna cewa zai fi son kada ya tsaya takara maimakon shiga tikitin da yake ganin zai sha kaye.
Babachir Lawal ya fara tone-tone
An ji cewa Babachir David Lawal ya yi zargin cewa wasu ‘yan takarar gwamna a NDC na aiki ne domin karya Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.
Ya bukaci magoya bayan NDC su yi watsi da abin da ya kira dabarun ‘yan jam’iyyar masu neman kawo cikas a Arewa maso gabas.
Babachir ya ce Aisha Dahiru-Binani tana tare da Atiku Abubakar, amma ya wanke su Mohammed Sani Yahaya da Babayo Ardo.
Asali: Legit.ng

