An Tara Malamai a Masallaci Sun Yi wa Tinubu Addu'a a Sokoto
- Gwamnatin jihar Sokoto ta sake gudanar da wata addu'a ta musamman domin samun ci gaban tattalin arziki a Najeriya, tare da zaman lafiya tsakanin al'ummomin kasar
- Malaman da suka jagoranci addu'ar sun kuma roki Allah ya ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Ahmed Aliyu nasara a zaben 2027
- Addu'ar ta gudana ne a Masallacin Gidan Gwamnati da ke Sokoto, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen bikin cika shekaru 66 da samun 'yancin kan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Gwamnatin jihar Sokoto ta gudanar da addu'a ta musamman domin neman Allah ya kawo ci gaba a Najeriya, musamman a bangaren tattalin arziki da siyasa, tare da tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'ummomin kasar.
An gudanar da addu'ar ne a Masallacin Gidan Gwamnati da ke Sokoto, a matsayin wani bangare na ayyukan bikin cika shekaru 66 da samun 'yancin kan Najeriya.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan jihar Sokoto, Abdullahi Bawa ne ya wallafa hotunan taron da malaman suka yi a wani sako da ya wallafa a Facebook.
Malamai sun yi addu'a ga Najeriya
Ma'aikatar Ayyuka na Musamman ta jihar ce ta shirya taron addu'ar, inda Sarkin Malaman Sokoto, Sheikh Yahaya Na Malam Boyi, ya jagoranci malamai shida wajen gudanar da ibadar.
Malaman sun roki Allah ya kawo karshen manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta, musamman matsalar rashin tsaro da wahalhalun tattalin arziki.
Sun kuma roki Allah ya ba kasar zabe mai zaman lafiya da nasara a shekarar 2027, tare da kare shugabannin kasar da yi musu jagora.
An yi wa Tinubu addu'ar nasara
A yayin addu'ar, malaman sun roki Allah ya ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Sokoto Ahmed Aliyu nasara a zaben 2027.
Sun kuma yi wa Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar, da shugaban APC na jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, da sauran shugabannin kasar addu'ar samun kariya da albarka.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027
Gwamna Ahmed Aliyu, wanda Sakataren Gwamnatin jihar, Muhammad Bello Sifawa, ya wakilta, ya gode wa malaman bisa amsa gayyatar gwamnatin jihar da kuma yin addu'a ga Najeriya.

Source: Facebook
Gwamnan ya bukaci malaman da su ci gaba da yi wa Najeriya addu'a, musamman a karshen wa'azozinsu da sauran koyarwarsu, domin kasar ta kai matsayin da ya dace da ita a tsakanin sauran kasashe.
Ya kuma gode wa malaman da al'ummar jihar Sokoto bisa ci gaba da yi wa gwamnatinsa addu'a, inda ya bukace su da su kara kaimi wajen hakan.
Malamai sun soki Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa wasu malaman addinin Musulunci daga jihohin Arewa sun gudanar da wani taro a jihar Kano inda suka bayyana matsayar da suka dauka kan zaben shugaban kasa na 2027.
Rahotanni sun ce akalla malamai 1,000 ne suka halarci taron ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026, inda suka ce sun yi nazari kan yadda ake tafiyar da kasar kafin su bayyana adawa da tazarcen Tinubu.
Malaman sun bayyana rashin amincewarsu da wasu manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, ciki har da janye tallafin man fetur da sauran sauye-sauyen da suka ce sun kara wa talakawa wahala.
Asali: Legit.ng
