Gwamna Ya Shiga Aikin da ba Nasa ba , Ya Fadi Abubuwa 3 da Suka Jawo Hatsarin Jirgin Sojoji

Gwamna Ya Shiga Aikin da ba Nasa ba , Ya Fadi Abubuwa 3 da Suka Jawo Hatsarin Jirgin Sojoji

  • Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ce matsalar fasaha ko na’ura na iya zama sanadin faduwar jirgin sojin saman Najeriya a Igbokoda
  • Aiyedatiwa ya ce yiwuwar matsalar yanayi ba ta da yawa, domin da an san yanayin ba shi da kyau da ba za a tashi da jirgin ba tun farko
  • Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce mutane 32 ne ke cikin jirgin, ciki har da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgi bakwai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo, Nigeria - Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya fara hasashen matsalolin da ka iya zama sanadin faduwar jirgin rundunar sojojin Najeriya, wanda ya yi hadari a yankin kauyen Igbokoda

Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana cewa matsalar fasaha ko ta na’ura da kuma yankewar sadarwa da hasumiyar kula da jiragen sama na iya zama sanadin hatsarin jirgin sojin saman Najeriya.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Ondo bayan mummunan hatsarin jirgin sama da ya kashe mutane

Gwamna Aiyedatiwa.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa yana magana a wurin taro Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Source: Twitter

Yadda jirgin sojojin ya fado a Ondo

Aiyedatiwa ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da Channels Television a shirin Politics Today, sa’o’i bayan da jirgin helikwafta ATR-42 ya yi hatsari a yankin Igbokoda da ke karamar hukumar Ilaje a jihar Ondo.

Jirgin yana kan hanya ne daga Benin zuwa Legas lokacin da ya fadi a wani yanki mai fadama da ke gaban sansanin sojojin ruwa a Igbokoda.

Daga bisani Rundunar Sojin Saman Najeriya ta fara aikin ceto da neman wadanda ke cikin jirgin.

Abubuwan da suka jawo hatsarin

Gwamna Aiyedatiwa ya ce mai yiwuwa jirgin ya samu matsala yayin da yake cikin iska, lamarin da ya haddasa yanke sadarwa tsakaninsa da hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama.

“Ba batun cewa suna son sauka ba ne kamar yadda na fada. Don haka, wata irin matsalar fasaha na iya faruwa da jirgin da ta sa ya rasa sigina.

Kara karanta wannan

Hadarin jirgin sojoji: Za a yi kwana 3 ana zaman makoki a fadin Najeriya

"Komai na iya faruwa ta fuskar matsalar na’ura; ba batun yanayi ba ne domin da yanayin ne matsalar, da ba za su tashi da jirgin ba tun farko, ko kuma watakila yanayi ya canza bayan sun tashi.
“Daga abin da muka ji, tafiyar ba ta da nisa sosai daga Benin zuwa Legas ba. Don haka, da yanayin ya kasance ba shi da kyau, da ba za su tashi da jirgin ba tun farko, za su jira har sai yanayin ya daidaita.
"Saboda haka, mai yiwuwa wata matsala ta samu jirgin yayin da yake cikin tafiya, lamarin da ya sa suka rasa sigina daga hasumiyar kula da jiragen sama, sannan wani abu ya samu matsala.”

- In ji Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo.

Jirgi.
Wani bangaren jirgin saman sojojin Najeirya da ya rikito a jihar Ondo Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Gwamnan Ondo ya ce babu wanda ya tsira

Kun ji cewa Gwamna Aiyedatiwa ya ce har yanzu ba a gano ko da wani mutum daya da ya tsira ba bayan hatsarin jirgin sojan sama da ya hallaka mutane da dama a jihar Ondo ba.

Aiyedatiwa ya ce mazauna yankin, jami’an ceto da jami’an tsaro sun gudanar da bincike a wurin hatsarin, amma ba su gano wanda ya tsira ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262