An Zo Wajen: INEC za Ta Fadi Makomar Takarar Pantami da Wasu 'Yan Siyasa

An Zo Wajen: INEC za Ta Fadi Makomar Takarar Pantami da Wasu 'Yan Siyasa

  • Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta bayyana matsayarta kan makomar wasu ‘yan takara da hukuncin Kotun Koli kan tsarin zaben fidda gwani ya shafa
  • Daga cikin ‘yan siyasar da ake ta ce-ce-ku-ce kan makomarsu akwai Farfesa Isa Ali Pantami a Gombe, Muhammad Nami a Neja, Mohammed Adamu a Nasarawa
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, zai yi wa manema labarai bayani a yau Talata, inda ake sa ran zai yi karin haske kan hukuncin Kotun Koli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar Zabe ta Kasa, INEC, za ta bayyana matsayarta kan wasu ‘yan takarar jam’iyyun siyasa da ake ganin hukuncin Kotun Koli kan zaben fidda gwani na iya shafa.

Ana sa ran INEC za ta bayyana matsayarta ne a yau Talata, bayan da hukumar ta samu kwafin hukuncin Kotun Koli da aka tabbatar da ingancinsa.

Kara karanta wannan

Abin ya zo: INEC za ta fara raba katunan PVC ga waɗanda suka cancanta kafin zaben 2027

Sheikh Isa Ali Pantami IGP Mohammed Adamu
Sheikh Isa Ali Pantami a hagu da tsohon IGP Mohammed Adamu a dama. Hoto: Abba Sani Pantami| Mohammed Adamu
Source: Facebook

Hukuncin da ya jawo ce-ce-ku-ce

Daily Trust ta wallafa cewa Kotun Koli ta tabbatar da ingancin wasu sassa na Dokar Zabe ta 2026 da suka shafi rajistar mambobin jam’iyyu da tsarin tsayar da ‘yan takara a zaben fidda gwani.

Kotun ta mayar da sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2) na dokar bayan Kotun Daukaka Kara ta soke su a wani hukunci da ta yanke a baya.

Sashe na 77(5) ya tanadi cewa ‘yan jam’iyya da sunayensu ke cikin rajistar da aka gabatar wa INEC a kalla kwanaki 21 kafin zaben fidda gwani ne kawai za su iya kada kuri’a ko neman takara a zaben.

Haka kuma, sashe na 77(6) ya bukaci jam’iyyu su yi amfani da rajistar da suka gabatar wa INEC a lokacin zaben fidda gwani, yayin da sashe na 77(7) ya tanadi hukuncin jam’iyyar da ta gaza gabatar da rajistar a lokacin da aka kayyade.

Batun makomar Pantami

Kara karanta wannan

Saura kwana 100 zabe: INEC za ta yi wa 'yan Najeriya bayani kan takarar 2027

A Gombe, ana nuna damuwa kan makomar Farfesa Isa Ali Pantami bayan sauya shekarsa daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Wasu mazauna Gombe na ganin cewa lokacin da Pantami ya fice daga APC ya shiga PDP na iya zama abin dubawa bisa tanadin dokar zabe da hukuncin Kotun Koli.

Sai dai wani jigo a PDP ya ce hukuncin Kotun Koli ya tabbatar da tsarin dokar ne kawai, ba tare da kotun ta yanke wani hukunci kai tsaye cewa Pantami bai cikin rajistar PDP ba ba.

Ya kuma yi nuni da cewa Kotun Tarayya ta soke zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 26 ga Mayu tare da bayar da umarnin sake gudanar da shi, wanda aka sake yi a ranar 29 ga Satumba.

Batun Nami da IGP Adamu

A jihar Neja, an kuma fara tambayar makomar Muhammad Nami, dan takarar gwamna na PDP a zaben 2027.

Wani lauya mai fashin baki kan kundin tsarin mulki da ke Minna, Barrista Abdulmumin Jibril Abdullahi, ya ce hukuncin Kotun Koli na iya sa a sake duba cancantar Nami.

Kara karanta wannan

Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027

Masu goyon bayan APC sun yi ikirarin cewa Nami ya kasance mai neman takarar sanata a APC a shekarar 2026 kafin daga bisani PDP ta tsayar da shi takarar gwamna a ranar 29 ga Agusta, 2026.

Shugaban hukumar INEC
Shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

A Nasarawa kuma, an samu ce-ce-ku-ce kan takarar tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu, wanda aka maye gurbinsa da tsohon dan takarar gwamna na SDP, Adamu Angba, bayan janyewarsa daga takarar.

Amupitan zai yi wa ‘yan Najeriya bayani

A wani labarin, kun ji cewa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, zai jagoranci wani taron manema labarai na duniya a Abuja a yau Talata, 6 ga Oktoba, 2026.

An shirya taron ne a daidai lokacin da aka fara kirga kwanaki 100 zuwa babban zaben 2027, inda INEC za ta yi bayani kan shirye-shiryenta, rajistar masu zabe da kuma batutuwan da suka shafi ‘yan takara.

Ana sa ran batun hukuncin Kotun Koli da makomar ‘yan takarar da ake ganin tanadin dokar ya shafa zai kasance cikin muhimman batutuwan da za a yi karin bayani a kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng