'Kamar Uba na yake' Bello Matawalle Ya Yi Magangun ban Mamaki kan Tinubu
- Karamin Ministan Tsaron Najeriya kuma tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya ce ya yarda da salon mulkin shugaban kasa Bola Tinubu
- Bello Matawalle ya bayyana cewa shugaban kasa Tinubu kamar uba yake a gare shi kuma zai tsaya wajen ganin ya yi nasara a 2027
- Ya bayyana cewa Tinubu ya kawo sauyi sosai, ana ba gwamnoni kudi sosai, ana shimfida tituna kuma saboda haka ne zai mara masa baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya kafa kungiyar 'Tinubu Again' domin tallata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da tattauna batun zaben shugaban kasa na 2027, inda 'yan siyasa ke neman goyon bayan jama'a.

Source: Twitter
Bello Matawalle ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da tashar RFI Hausa a Facebook, inda ya ce shugaba Tinubu kamar uba yake a wajen shi.
'Tinubu zaman uba yake gareni'
Yayin da yake bayani game da alakar shi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Bello Matawalle ya ce ya dauki shugaban kasar a matsayin uba.
Ya ce:
'Tinubu zaman uba yake a gare ni'
Ministan tsaron ya kara da cewa mutum ne wanda zai iya tsaya maka matukar kuna tare, ya ce mutum ne idan kana tare da shi ba zai baka kunya ba.
'Yadda Tinubu zai tsaya maka, karshenta in dan Arewa ne dan uwan ka ba zai tsaya maka ba'
A kan haka Bello Matawalle ya ce duk abin da zai yi yaga Tinubu ya samu nasara a 2027 ya yi saboda halin shugaban kasar.
Ya ce zai cigaba da aiki da duk wadanda suka yi aiki tare domin kawo nasarar APC zaben 2027 a dukkan matakai.
Batun kungiyar Tinubu Again
Bello Matawalle ya ce zai cigaba da tallata Tinubu a karkashin kungiyar 'Tinubu Again' saboda yadda ake ba gwamnoni suna ayyuka.

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu
A bangaren ayyuka, Bello Matawalle ya bayyana cewa yanzu haka ana titin Sokoto zuwa Legas, wanda tun lokacin Sardauna aka so a yi shi amma ba a yi ba.

Source: Twitter
Ya ce kungiyar aikinta shi ne ta shiga lungu da sako domin sanar da jama'a ayyukan da Tinubu ya yi, da wayar da kan jama'a kan irin abin da 'yan adawa ke fada.
Ya ce kungiyar za ta fede biri har wutsiya game da ayyukan Bola Tinubu domin a sake zaben shugaba kasa da sauran 'yan APC.
Magana kan rashin tsaro
Bello Matawalle ya ce an samu nasara sosai a kan rashin tsaro, sai dai ya ce ba lallai a fito da komai a bainar jama'a ba.
Ya ce ya sha fada a baya cewa idan aka shawo kan matsalar tsaro a Zamfara to kusan an magance dukkan matsalar a Najeriya.
Yayin da ya ke korafi kan rashin samun hadin kan gwamnatin tarayya a baya, ya ce a lokacin da yake gwamna ba shi iya samun ministan tsaro a waya su yi magana, sabanin yadda ake aiki yanzu.
A karshe ya yi kira ga 'yan Najeriya da kada su yadda da 'yan adawa su yaudare su, inda ya ce kusan duk daya suke, ya ce yaudarar su kawai ake son yi.
An yi wa Tinubu addu'a a Sokoto
A wani labarin, mun kawo muku cewa an yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu addu'a domin samun nasara a jihar Sokoto.
Rahotanni sun nuna cewa an tara malamai ne a masallacin gidan gwamnatin jihar Sokoto yayin murnar cikar Najeriya shekara 66.
Malaman addinin da aka tara sun yi wa gwamna Ahmed Aliyu Sokoto addu'o'i na musamman da kuma rokon Allah ya kawo sauki a Najeriya.
Asali: Legit.ng

