Tura Ta Kai Bango: Mutane Sun Yi Zanga Zanga, an Tare Babbar Hanyar Niger
- Wasu ’yan yankin Mokwa ta sa aka toshe babbar hanyar Mokwa-Bida, bayan zargin yawaitar garkuwa da mutane da ’yan bindiga ke yi
- Masu zanga-zangar sun ce an sace mazauna 15 a baya-bayan nan, kuma jami’an tsaro ba su samu nasarar ceto su ba
- Toshe hanyar ya jefa matafiya cikin wahala, inda wasu suka shafe sama da sa’o’i biyar a Mokwa suna jiran gwamnatin ta kawo mafita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Mokwa, Niger - Matafiya da masu amfani da babbar hanyar Mokwa-Bida a Niger sun shiga mawuyacin hali da ake ciki a yankin.
Rahotanni sun masu zanga-zanga sun toshe hanyar saboda zargin yawaitar hare-haren ’yan bindiga.

Source: UGC
Wani wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) da ya isa wurin ya ruwaito cewa masu zanga-zangar sun toshe dukkan hanyoyin shiga garin Mokwa.
Muhimmancin da hanyar ke da shi
Babbar hanyar Mokwa-Bida muhimmiyar hanyar tarayya ce mai tsawon sama da kilomita 100, wadda ke haɗa masu ababen hawa daga Kudu maso Yamma zuwa Arewacin Najeriya.
Bayanan da aka tattara sun nuna cewa matafiya da dama sun makale a wurin tun daren Asabar, saboda rashin damar wucewa ta hanyar.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, Saliu Mohammed, ya yi zargin cewa wasu ’yan bindiga da ake zargi sun sace mazauna 15 na yankin a baya-bayan nan.
Mohammed ya kuma yi zargin cewa jami’an tsaro ba su samu damar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su ba.
Ya ce masu zanga-zangar za su ci gaba da toshe hanyar har sai an ceto mutanen da aka sace.

Source: Original
Abin da matafiya ke cewa kan lamarin
Wata matafiya mai suna Joy Amaechi, wadda ke tafiya daga Ilorin zuwa Abuja, ta bayyana irin wahalar da ta fuskanta sakamakon toshewar hanyar.
Amaechi ta ce ta shafe kusan sa’o’i biyar a Mokwa ba tare da samun mafita ba, inda ta yi kira ga gwamnati ta gaggauta shiga tsakani.
Wani direban kamfanin sufuri na jama’a, Henry Nwachuckwu, ya ce ya isa Mokwa da misalin ƙarfe 7 na safe ranar Lahadi, cewar Punch.
Ya bayyana cewa har zuwa lokacin da aka tattara rahoton, da misalin ƙarfe 10:30 na safe, masu zanga-zangar ba su bar babbar hanyar ba.
Toshewar hanyar ta haifar da cunkoso da tsaiko ga matafiya da direbobi, lamarin da ya ƙara tsananta wahalar da jama’a ke fuskanta sakamakon matsalar tsaro.
Masu zanga-zangar sun buƙaci hukumomin gwamnati da jami’an tsaro su gaggauta ɗaukar mataki domin ceto mutanen da ake zargin an sace tare da tabbatar da tsaron yankin.
Hanyar Mokwa-Bida na da matuƙar muhimmanci ga zirga-zirgar jama’a da jigilar kayayyaki tsakanin sassan Kudancin Najeriya da Arewa.
Rashin tsaro: An toshe hanya a Abuja
Kun ji cewa masu zanga-zanga sun toshe gadar Karu-Nyanya, sun bukaci gwamnati ta dauki mataki kan yawaitar hare-haren yan ta'adda a kasar nan.
Hakan dai na zuwa ne yayin da zanga-zangar adawa da matsalar rashin tsaro ta shiga rana ta uku a babban birnin tarayya Abuja.
Sha'anin tsaro na ci gaba da kara kamari a Najeriya musamman bayan sace dalibai da malamai a makarantu a jihohin Oyo da Borno.
Asali: Legit.ng


