Trump Ya Jawo Magana a Kamfe, Ya Ce Zai Bari Iran Ta ‘Babbake’ Birane 2 a Amurka
- Donald Trump ya ce Iran za ta iya “kai wa” Los Angeles da San Diego hari, yayin da kalaman suka jawo suka
- Gwamnan California Gavin Newsom ya bayyana Trump a matsayin mutum mai hatsari, yana zargin shugaban da goyon bayan farmakin
- Trump ya yi kalaman ne yayin gangamin siyasa a Nebraska, amma ba a bayyana ko akwai wani rahoton leken asiri ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Donald Trump ya bayyana cewa Iran za ta iya “kai wa” Los Angeles da San Diego hari, a wani jawabin da ya yi yayin gangamin siyasa.
Trump ya ce yana son ganin gagarumar nasara a zaben watan Nuwamba, yana mai cewa idan ya zama dole, kasar Iran ta kai hari birni.

Source: Getty Images
Ya kara da cewa wannan zai kasance karamin abu domin tabbatar da tsaron duniya da na Amurka, lamarin da jama’ar wurin suka yi wa murna, cewar Al Jazeera.
Gwamna ya caccaki Trump kan kalamansa
Kalaman Trump sun jawo suka daga shugabannin California, ciki har da Gwamna Gavin Newsom, wanda ya bayyana shugaban da cewa “mahaukaci ne kuma mai hatsari.”
Newsom ya ce Trump yana goyon bayan harin da makiya kasashen waje za su kai kan Los Angeles, yana mai cewa hakan ba abu ne na al’ada ba.
Magajin garin San Diego, Todd Gloria, ya ce birnin ba zai zama abin sadaukarwa ba, yana mai cewa ba za a dauke shi a matsayin karamin farashi ba.
Trump ya yi kalaman ne a cikin wani dogon jawabi, inda ya kuma yi magana kan farashin man fetur, Venezuela da kuma sukar kafafen yada labarai.
Sai dai ba a bayyana ko kalaman Trump sun samo asali ne daga wani rahoton leken asiri ba, kuma Iran ba ta da wata cikakkiyar damar kai harin makami mai linzami Amurka.

Source: Twitter
Gargadin da hukumomi suka taba yi
Hukumomin tsaro a California sun taba gargadin jama’a cewa yakin Iran na iya haifar da harin jiragen sama marasa matuki a jihar.
Amma majiyoyi sun shaida cewa babu wani ingantaccen bayanin sirri da ke nuna cewa irin wannan hari zai faru, kuma jami’ai ba su dauki gargadin da muhimmanci ba.
Trump ya dade yana da rashin kyakkyawar alaka da Los Angeles, inda a baya ya fuskanci matsaloli wajen samun karbuwa ga harkokin kasuwancinsa.
A shekarar 2019, Trump ya ziyarci San Diego domin nuna goyon baya ga shirin gina katangar iyakar Amurka da Mexico, cewar Los Angeles Times.
Magajiyar garin Los Angeles, Karen Bass, ta ce kalaman Trump suna da hatsari, kuma za su iya jefa tsaron al’umma cikin hadari.
Ta ce aikin shugaban kasa shi ne kare kasa, ba wai ya yi barazana ga kasar ko kuma ya karfafa kai hare-hare kan rayukan Amurkawa ba.
Sanata Adam Schiff daga California shi ma ya soki Trump, yana tambayar sau nawa shugaban zai ci gaba da cewa yakin Iran zai kare nan ba da jimawa ba.
Xavier Becerra, dan takarar jam’iyyar Democrat da ke kan gaba a takarar gwamnan California, ya ce bai kamata a yi wasa da rayukan miliyoyin mazauna Los Angeles da San Diego ba.
Sharudan Iran 7 da ta gindaya ga Amurka
Mun ba ku labarin cewa Iran ta ce ba za ta sake buɗe mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta cika wasu sharudda bakwai da aka cimma.
Kakakin Majalisar Iran, Mohammad Baqer Ghalibaf, ya ce Tehran ta yi watsi da matsin lambar Amurka, tana mai dagewa kan sharuɗɗanta.
Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce za a iya buɗe mashigar cikin kwanaki bakwai idan Amurka ta amince da sharuɗɗan.
Asali: Legit.ng


