Musulunci Ya Yi Rashi, Sakataren Majalisar Shari'a Ta Najeriya Ya Rasu
- Babban Magatakardar Majalisar Koli ta Tabbatar da Shari’a a Najeriya, Malam Nafi’u Baba Ahmad, ya rasu da safiyar Talata
- An sanar da rasuwar malami kuma lauya a yau Talata, inda aka bayyana cewa za a yi jana’izarsa da karfe 1:30 na rana a Abuja
- Rasuwarsa ta jefa al’ummar Musulmi cikin jimami, musamman wadanda suka san ayyukansa a fannin ilimi, Shari’a da kare muradun Musulman Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mal. Nafi’u Baba Ahmad, mni, Babban Magatakardar Majalisar Koli ta Tabbatar da Shari’a a Najeriya, ya rasu da safiyar Talata.
Sanarwar rasuwarsa ta bayyana cewa za a gudanar da jana’izarsa da karfe 1:30 na rana a Masallacin Kasa da ke Abuja.

Source: Facebook
Shugaban Sunnah TV, Dr Ibrahim Disina ne yasanar da rasuwar marigayin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Wane ne Nafi'u Baba Ahmed?
Malam Nafi’u Baba Ahmad ya kasance malamin addinin Musulunci, lauya kuma masani da harkokin kasa da al’umma.
Ya samu tarbiyyar ilimin addinin Musulunci tun yana karami, inda ya yi karatun Alkur’ani, harshen Larabci, fikihu da sauran ilimomin Musulunci a wajen malamai.
Daga bisani ya karanci shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, abin da ya ba shi damar hada ilimin addini da na zamani wajen tattauna batutuwan Shari’a, kundin tsarin mulki da harkokin shugabanci.
Mukaman da Nafi'u Baba Ahmed ya rike
A matsayinsa na Babban Magatakardar Majalisar Koli ta Tabbatar da Shari’a a Najeriya, Malam Nafi’u ya kasance cikin jagororin gudanar da harkokin majalisar da daidaita ayyukanta.
Ya rika hada kan shugabannin majalisar da sauran bangarorin da ke aiki da ita, tare da shiga tattaunawa kan batutuwan da suka shafi addini, hakkokin Musulmi da al’amuran kasa.
Haka kuma, ya kasance cikin masu bayar da gudunmawa wajen tsara manufofi da matsayar majalisar kan batutuwan da suka shafi Shari’a, adalci, ’yancin addini da ci gaban al’umma.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027
Gudunmuwar da Nafi'u ya bayar
Malam Nafi’u ya yi suna wajen rubuce-rubuce da jawabai kan shugabanci, adalci a cikin al’umma, dangantakar mabiya addinai da kuma matsayin addini a harkokin jama’a.
Ya kuma kasance cikin masu bayyana fahimta kan batutuwan Shari’a da tsarin mulkin Najeriya, tare da kokarin fayyace matsayin Musulunci a cikin al’umma mai mabiya addinai daban-daban.
A shekarun rayuwarsa, ya ci gaba da ba da gudunmawa wajen bunkasa ilimi, kare hakkokin addini da karfafa cibiyoyin Musulunci a Najeriya.

Source: Original
An karrama shi da mni
Shafi majalisar shari'a ta kasa ya wallafa cewa an karrama Nafi’u Baba Ahmad da matsayin mamba na mni na NIPSS, Kuru.
Wannan matsayi ya kara nuna gudunmawarsa wajen tattaunawa kan manufofin kasa, shugabanci da ci gaban Najeriya.
Rasuwarsa ta zo ne a lokacin da yake ci gaba da gudanar da ayyukansa na jagoranci da hidima ga al’ummar Musulmi da kasa baki daya.
Ango ya rasu a Gombe
A wani labarin, mun ruwaito cewa Malam Habu, wani ango a Gombe, ya rasu a hatsarin mota yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa wajen da za a daura aurensa.

Kara karanta wannan
Kwana ya ƙare: Babban malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Yaakub ya rasu
Malam Habu ya rasu ne a ranar da aka shirya gudanar da daurin auren, lamarin da ya jefa iyalansa, abokansa da sauran al’umma cikin babban alhini.
An gudanar da jana’izarsa da jana’iza bisa tsarin Musulunci, inda ’yan uwa da abokan arziki suka taru domin yi masa addu’a da neman Allah Ya gafarta masa.
Asali: Legit.ng
