Latest
Kakakin Majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya yi murabus bayan ‘yan majalisa sun shirya tsige shi, kamar yadda mai taimaka masa ta tabbatar.
Tarayyar Turai ta ware €2.3m ga Najeriya da wasu ƙasashe uku domin yaƙi da annobar kwalara, inda Najeriya za ta samu €1.5m daga cikin jimillar kudin.
Shugaban matasan APC, Dayo Israel, ya ce rashin nasarar jam’iyyar a Osun ya kamata ya zama gargadi kafin 2027, tare da yin kira ga APC ta gyara kura-kurenta.
Bayan kwanaki 84 kacal ko makamancin haka Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje ya koma APC da ya yi murabus daga NDC a Kano. Abdulaziz ya koma layin mahaifinsa.
Dan takarar jam'iyyar PRP, Donald Duke, ya buƙaci ‘yan adawar Najeriya su binne son zuciya, su haɗa kai domin kayar da APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A baya, mun wallafa cewa dakarun sojin Najeriya sun gano cewa akwai sauran yan ta'adda da ke rakabe a kusa da kauyen jihar Sokoto bayan wani hari.
Rundunar ‘yan sandan Kebbi ta samu nasarar kama wata mata, Khadija Ibrahim mai shekaru 19 kan zargin satar jariri a Zuru tare da kai shi wurin mijinta.
A labarin nan, za a ji cewa Najeriya ta bayyana cewa ta yi shirin fara kera makaman da za ta yi amfani da su wurin fatattakar yan ta'adda da suka addabi jama'a.
Hukumar kashe gobara ta tabbatar da mutuwar leborori 4 da dalibar Islamiyya daya sakamakon ruftawar wasu gine-gine biyu a kananan hukumomi 2 a Kano.
Masu zafi
Samu kari