Minista Ya Yi Barazanar Hada Yan Kwangila da EFCC, Ya ba Su Wa’adin Awa 72

Minista Ya Yi Barazanar Hada Yan Kwangila da EFCC, Ya ba Su Wa’adin Awa 72

  • Ministan Ayyuka a gwamnatin Bola Tinubu ya yi barazanar hada yan kwangila da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC a Najeriya
  • Dave Umahi ya bai wa masu kwangilar gyaran hanyar Abuja zuwa Lokoja wa'adin sa'o'i 72 su koma aiki ko su fuskanci matsala
  • Ya ce gwamnatin Tinubu ta saki kuɗin aikin, tare da alƙawarin hukunta sakaci da jinkiri wajen ayyuka saboda ba wasa aka zo yi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bai wa masu kwangilar da ke aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Lokoja wa'adin sa'o'i 72.

Ya umarce su da su tattara kayan aiki da ma'aikata su koma wurin aiki ko kuma su fuskanci hukunci.

Minista ya yi barazana ga yan kwangila
Ministan ayyuka a Najeriya, Dave Umahi. Hoto: @DaveUmahi.
Source: Twitter

Ministan ya yi wannan jawabi ne yayin duba aikin hanyar tare da kwamitocin ayyuka na Majalisar Tarayya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Haka aka yi wa Jonathan': Malami ya hango makarkashiya ga Tinubu a 2027

Gargadin Ministan ayyuka ga yan kwangila

Umahi ya yi gargadin cewa ba za a ƙara lamuntar masu kwangilar da suka karɓi kuɗin gwamnati ba tare da cika alkawari ba.

Ya ce:

"Idan kuna riƙe da kuɗin gwamnatin tarayya, ku fito da su ku yi aikin, ko kuma mu fara kai ƙara wajen 'yan sanda da Hukumar EFCC domin ɗaukar matakin da ya dace."

Ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya riga ya amince da sakin kuɗaɗen aikin domin ci gaba da aiwatar da shi.

Umahi ya buƙaci masu kwangilar da abin ya shafa su gaggauta tura injuna da ma'aikata zuwa wurin aiki.

Tsohon gwamnan na Ebonyi ya kuma yi alƙawarin hukunta jami'an Ma'aikatar Ayyuka da suka gaza sa ido yadda ya kamata kan ayyuka.

Minista ya fadi yadda Tinubu ke aikin hanyoyi a Najeriya
Tsohon gwamnan Ebonyi kuma Ministan ayyuka a Najeriya, Dave Umahi. Hoto@DaveUmahi.
Source: Getty Images

Minista ya ba yan kwangila wa'adin awa 72

A cewarsa, ba za a amince da sakaci, jinkiri ko yin aiki maras inganci da zai kawo cikas ga ci gaban ƙasa ba, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: An hallaka mawaki dan asalin Najeriya a Burtaniya

"Ina ba ku wa'adin sa'o'i 72 ku tattara kayan aiki da ma'aikata yadda ya kamata ku koma wannan hanya, ku yi amfani da kuɗin da aka ba ku wajen aiwatar da aikin. Shugaban Ƙasa ya amince cikin karamci da sakin kuɗaɗen aikin, kuma wajibi ne kowa da ke da hannu a ciki ya cika nauyin da ya rataya a wuyansa."

- Dave Umahi

Sai dai ya yaba da ci gaban da aka samu a wasu sassan aikin, yana mai tabbatar da biyan basussukan da ake bi.

Ya kuma nuna damuwa kan lalacewar hanyar zuwa Abuja, yana gargadin cewa za ta iya zama ba ta biyuwa cikin watanni idan ba a gaggauta gyaranta ba.

'Tinubu ya yi wa Arewa gata' - Umahi

Mun ba ku labarin cewa Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce kaso mafi tsoka na manyan ayyukan titunan gwamnatin Bola Tinubu suna Arewacin Najeriya.

Umahi ya bayyana cewa rabon ayyukan ya nuna gwamnati na kokarin tabbatar da ci gaba mai daidaito a fadin kasa na don kai.

Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce aikin babbar hanyar Gombe zuwa Biu zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da hada yankuna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.