Sabon Mafi Karancin Albashi da Ake So Gwamnati Ta Rika Biyan Sojojin Najeriya

Sabon Mafi Karancin Albashi da Ake So Gwamnati Ta Rika Biyan Sojojin Najeriya

  • Tsohon Manjo Janar John Enenche ya ce bai kamata a rika biyan sojan Najeriya kasa da ₦250,000 a wata ba saboda tsadar rayuwa
  • Enenche ya bayyana cewa albashin ₦100,000 da gwamnati ta amince da shi bai wadatar ba idan aka yi la’akari da nauyin aikin soja
  • Ab ce sojojin Najeriya na karbar albashi kasa da takwarorinsu a kasashe da dama na Afirka kamar Afirka ta Kudu, Kamaru da Senegal

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja – Tsohon Manjo Janar John Enenche (mai ritaya) ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake duba albashin sojojin Najeriya, inda ya ce ya kamata mafi ƙarancin albashin soja ya zama aƙalla N250,000 a wata.

Enenche ya bayyana cewa albashin da ake biya a halin yanzu bai dace da irin sadaukarwar da sojoji ke yi ba, musamman duba da yadda tsadar rayuwa ke ƙaruwa a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

An fallasa kuskuren gwamnatin tarayya da ya karfafa ayyukan Boko Haram a Arewa

Tsohon Manjo Janar John Enenche ya ce albashin sojoji na N100,000 ya yi kadan.
Manjo Janar John Enenche (mai ritaya) da ya ce albashin sojoji ya yi kadan. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Yadda batun albashin sojoji ya sake tasowa

Batun walwalar sojoji ya sake ɗaukar hankalin jama'a ne bayan Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa an ƙara mafi ƙarancin albashin soja daga N49,000 zuwa N100,000 a wata, in ji rahoton Daily Trust.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa duk da wannan ƙarin, har yanzu sojojin Najeriya na karɓar albashi ƙasa da takwarorinsu a ƙasashe da dama na Afirka.

Bincike ya nuna cewa sojoji masu ƙaramin muƙami a ƙasashe irin su Afirka ta Kudu, Kenya, Gambiya, Togo, Nijar, Benin, Senegal da Kamaru na samun albashin da ya fi na Najeriya nesa ba kusa ba.

"N250,000 ma bai yi yawa ba" – Enenche

Da yake magana a wata hira da tashar Arise TV, Enenche ya ce ko N250,000 da yake ba da shawara a matsayin mafi ƙarancin albashi ba yawa ba ne idan aka yi la'akari da halin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

An ayyana neman wani sojan Najeriya ruwa a jallo, an saki hotuna da bayanansa

Ya ce kuɗin sufuri, abinci da sauran buƙatun yau da kullum sun yi tsada matuƙa, yana mai misalin cewa a Abuja kuɗin tafiya guda na iya kaiwa tsakanin N1,000 zuwa N2,000.

Tsohon shugaban ya yi watsi da ra'ayin cewa samar wa sojoji masauki, kayan aiki da makamai na iya maye gurbin ƙarin albashi.

A cewarsa, soja mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa ga ƙasa, kuma ba shi da damar gudanar da wata sana'a ko noma domin ƙara samun kuɗin shiga saboda yanayin aikinsa.

Ya ƙara da cewa sojoji na kan aiki a kowane lokaci, abin da ya bambanta su da sauran ma'aikatan gwamnati.

An ce albashin sojojin Najeriya na N100,000 ya yi kadan, don haka akwai bukatar a kara masu.
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede a hedikwatar rundunar hadin gwiwa da ke Maiduguri a ranar 16 ga Maris, 2026. Hoto: Audu MARTE / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Masana sun ce walwalar sojoji na da muhimmanci

Kiran Enenche ya yi daidai da irin damuwar da jami'an soja masu aiki da masu ritaya suka dade suna nunawa kan yadda ƙarfin sayen albashin sojoji ke ci gaba da raguwa.

Masana harkokin tsaro sun sha bayyana cewa inganta walwala da albashin dakaru na daga cikin muhimman hanyoyin ƙara musu ƙwarin gwiwa, inganta ƙwarewa da kuma taimaka musu wajen yaƙi da ta'addanci, ƴan bindiga da sauran matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bani, Shugaba Tinubu ya fadada rundunar sojojin Najeriya

Juyin mulki ba zai yiwu a Najeriya ba

A wani labari, mun ruwaito cewa, Janar John Enenche mai ritaya ya yi magana kan yiwuwar juyin mulki a kasar da ke makwabtaka da Benin.

Janar John Enenche ya bayyana cewa juyin mulki yanzu kusan ya zama ba zai yiwu ba a Najeriya saboda fahimtar dimokuradiyya cikin sojoji.

Tsohon babban sojan ya ce horo da kwarewar da aka ba jami’an soja tun bayan mulkin Shugaba Janar Ibrahim Babangida sun canja tunaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com