Alkawarin Obi ga Kwankwaso kan Wa'adi 1 Ya Ci Gaba da Jawo Rudani a Arewa
- Yarjejeniyar wa'adi ɗaya tsakanin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ta fara jawo rarrabuwar kai a yankin Arewa
- Ƙungiyar ACF ta ce yarjejeniyar alamar neman mulki ne cikin gaggawa, yayin da wasu suka ce ya dace da tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin yankuna
- Lauyoyi sun bayyana cewa kundin tsarin mulki bai amince da irin yarjejeniyar ba, don haka ba ta da ƙarfin doka kuma ba za ta tilasta kowa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ana ci gaba da maganganu game da tikitin dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
Yarjejeniyar da Peter Obi, ya kulla da abokin takararsa Sanata Rabiu Kwankwaso na yin wa'adi ɗaya idan ya lashe zaɓe ya jawo muhawara daga ƙungiyoyin Arewa da manyan lauyoyi.

Source: Facebook
Alkawarin da Obi ya yi ga Kwankwaso
Kwankwaso ya tabbatar a wata hira da Channels Television cewa Obi ya rattaba hannu kan yarjejeniya a rubuce, wadda ta tanadi mika mulki ga Arewa bayan wa'adi ɗaya.
Obi ya yi alƙawarin yin wa'adi guda ɗaya kacal domin mutunta tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, ganin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana mulki daga Kudu.
Tsohon gwamnan Kano ya bayyana cewa yana da cikakken yaƙini Obi zai cika alƙawarinsa, yana mai cewa sun yi wannan yarjejeniya ne cikin amana da mutunta juna.
Sai dai ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi watsi da yarjejeniyar, tana mai cewa ba ta da tushe a kundin tsarin mulki kuma alamar matsananciyar neman mulki ce.
Sakataren yaɗa labarai na ACF, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya ce babu wanda ya ba Obi ko Kwankwaso ikon tattauna makomar shugabancin Najeriya tsakanin Arewa da Kudu.
A cewarsa, idan Obi ya zama shugaban ƙasa kuma ya yi aiki nagari, babu abin da zai hana shi neman wa'adi na biyu saboda kundin tsarin mulki ya ba shi damar hakan.

Source: Facebook
Obi/Kwankwaso: Ƙungiyoyi, lauyoyi sun magantu
A gefe guda, ƙungiyar Middle Belt Forum (MBF) ta ce ba ta da matsala da alƙawarin wa'adi ɗaya, muddin hakan zai ba yankin Middle Belt damar karɓar mulki a shekarar 2031.
Mai magana da yawun MBF, Luka Binniyat, ya ce tun farko sun goyi bayan ci gaba da mulki a Kudu zuwa 2031, sannan daga baya shugaban ƙasa ya fito daga yankin 'Middle Belt', cewar Punch.
Ƙungiyar ta kuma yi iƙirarin cewa tun 1999 Arewar Musulmi ta samu damar mulki sosai, don haka lokaci ya yi da ɗan takarar Kirista daga Middle Belt zai jagoranci ƙasar.
Manyan lauyoyi da suka yi magana kan batun sun ce irin wannan yarjejeniya ba ta da ƙarfin doka, domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince da wa'adin shekara huɗu da damar yin wa'adi biyu.
Babban lauya Abdul Balogun (SAN) ya ce doka ba ta tanadi irin wannan yarjejeniya ba, yayin da Hillary Omoh ta ce kowanne ɓangare na iya janye ba tare da hukunci ba.
Shi ma lauya James Ekwe ya ce duk wanda ya rattaba hannu kan irin wannan yarjejeniya zai dogara ne da mutuncinsa wajen cika alƙawarin, domin babu wata doka da za ta tilasta hakan.
Babachir ya fadi damar Obi da Kwankwaso
An ji cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana ra'ayinsa kan tikitin da zai iya lashe zaben shugaban kasa a 2027.
Babachir ya ce haɗakar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a takarar shugaban ƙasa za ta fi samun damar lashe zaɓen 2027 idan aka kwatanta da kowannensu ya tsaya shi kaɗai.
Ya yi hasashen cewa haɗakar Obi da Kwankwaso za ta samu kashi 70 cikin 100 na damar yin nasara, yayin da Shugaba Bola Tinubu zai samu kashi 50 cikin 100.
Asali: Legit.ng


