'Yan Bindiga 6 Sun Mutu yayin da Suka Yi Yunkurin Kai Hari a Jihar Zamfara
- Jami’an tsaro sun dakile wani mummunan harin ‘yan bindiga a yankin karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara
- Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta tabbatar da wannan nasara, ta ce an kashe ‘yan bindiga shida yayin musayar wuta
- Tuni dai aka kara girke dakaru a yankin domin tabbatar da zaman lafiya da kuma dakile duk wani yunkuri da ka iya biyo baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Jami’an tsaro sun samu nasarar dakile wani hari da ‘yan bindiga suka kai garin Kanoma da kauyen Gidan Daji a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 9 ga watan Yunin 2026, lokacin da dimbin ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suka kutsa yankunan domin kai hari.

Kara karanta wannan
Dalibai sun fara gudun neman tsira da wani malami ya yi shigar 'yan bindiga a makaranta

Source: Twitter
Jami’an tsaro sun gwabza da mahara
Daily Trust ta rahoto cewa a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya bayyana cewa maharan sun zo ne da miyagun makamai.
Kakakin yan sandan ya ce daga cikin makaman da aka gani a hannun yan bindigar akwai RPG, GPMG, bindigogin harbo jiragen sama da kuma AK-47.
Ya ce bayan jami’an tsaro sun samu kiran gaggawa, take suka yi hanzarin tura jami’ai zuwa yankin domin dakile harin.
Tawagar da aka tura ta kunshi ‘yan sanda na caji ofis din Maru, Operation Fansan Yamma, jami’an Violence Crime Response Unit (VCRU) da kuma masu aikin sa-kai na yankin karkashin jagorancin DPO na yankin.
An kashe ‘yan bindiga 6
Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun yi artabu mai zafi da maharan, lamarin da ya tilasta musu ja da baya tare da hana su cimma manufarsu.
“Jami’an tsaro sun fafata da maharan a musayar wuta, inda aka kashe ‘yan bindiga shida da ke kan babura biyu,” in ji sanarwar.
DSP Yazid ya kara da cewa wasu daga cikin maharan sun tsere zuwa cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga, cewar rahoton Tribune Nigeria.
'Yan sanda sun kara tsaurara tsaro
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko jikkata ko mutum daya daga cikin jami’an tsaro ko mazauna yankunan da abin ya shafa ba.
Haka kuma, an kara yawan jami’an tsaro a yankin tare da fara sintiri akai-akai domin tabbatar da zaman lafiya da kuma farautar wadanda suka tsere.

Source: Twitter
Rundunar ta sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kira ga mazauna yankin da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai a kan lokaci.
'Yan sanda sun kutsa dajin Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar yan sanda da wasu jami'an tsaro sun karbe iko da dajin Jangebe da ke jihar Zamfara bayan artabu da miyagun 'yan bindiga.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa an yi nasarar hallaka yan bindiga uku.
Rundunar ta ce an kwato kayayyaki da makamai da suka hada da bindigogi AK-47 guda uku, harsasai 23, magazines uku da kuma babura 10.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
