Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Soja da Wasu Sojoji 7 a Kaduna
- Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka tuba daga ayyukan ta'addanci a baya sun kashe sojoji takwas ciki har da wani Laftanan a Kaduna
- An ce sojojin sun fada komar 'yan bindigar ne yayin da suke kan hanyar zuwa kai daukin gaggawa a wasu yankunan Chikun da Igabi
- Harin ya sake tayar da kura kan tsarin Gwamnatin Najeriya na sulhu da 'yan bindiga da kuma na sake mayar da ‘yan bindiga cikin al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kaduna - Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin tubabbu ne sun kashe akalla sojoji takwas ciki har da wani Laftanan a jihar Kaduna.
An ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin yayin da sojoji ke kan hanyarsu ta zuwa kai daukin gaggawa bayan samun rahoton wani harin garkuwa da mutane da aka kai tsakanin kananan hukumomin Chikun da Igabi.

Source: Twitter
Yadda aka kashe sojoji 8 a Kaduna
Jaridar The Cable ta ce Zagazola Makama ya shaida mata cewa sojojin sun yi artabu da ‘yan bindigar ne yayin da suke kokarin hana sabon hari a yankin.
Rahoton ya ce maharan sun yi wa sojojin kwanton bauna inda aka kashe babban jami’i mai mukamin Laftanar tare da wasu sojoji bakwai.
Jaridar ta ce ta tuntubi rundunar sojin Najeriya domin jin ta bakinta kan lamarin amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu martani ba.
Iyalan sojoji sun tabbatar da lamarin
Wani dan uwan daya daga cikin sojojin da aka kashe ya tabbatar wa SaharaReporters faruwar lamarin ta sakon WhatsApp.
A cewarsa, iyalan mamatan na cikin jimami kuma har yanzu ba su samu wata sanarwa daga rundunar sojin Najeriya ba.
Majiyar ta ce:
“Eh, zan iya tabbatar da cewa 'yan bindiga, da ake ikirarin sun tuba, sun kashe sojoji takwas ciki har da dan uwana a Kaduna."

Kara karanta wannan
Fada ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a Kaduna, an kashe manyan jagorori 4
Ya kara da cewa bisa bayanan farko da suka samu, ‘yan bindigar na shirin kai hari wasu garuruwa ne da ke kusa da kogin Kaduna kafin su yi arangama da sojojin.

Source: Twitter
Ce-ce-ku-ce kan sulhu da 'yan bindiga
Sabon harin ya sake tayar da muhawara kan tasirin tsarin sulhu da Gwamnatin Kaduna da Gwamnatin tarayya ke yi da ‘yan bindiga domin dawo da zaman lafiya, in ji jaridar.
Gwamnati dai na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen tattaunawa da sake mayar da wadanda suka mika wuya cikin al’umma karkashin shirin Operation Safe Corridor da wasu tsare-tsare na jihohi.
Sai dai mutane da dama na nuna shakku kan tsarin tare da bayyana cewa yana fuskantar suka daga jama’a saboda yawaitar hare-hare duk da ikirarin cewa wasu ‘yan bindiga sun tuba.
Lakurawa sun kashe Sojojin Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, sojoji biyar sun mutu yayin da aka yi wata arangama tsakanin sojoji da 'yan ta'addar Lakurawa a yankin Gudu da ke Sokoto.
Rundunar sojojin Najeriya ta ce duk da asarar jami'anta, ta kashe 'yan ta'addar shida tare da kwace bindigogi da harsasai 160.
Sojoji sun nemi jama’a su kasance masu sanya ido, su kuma sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
