Tikitin Obi da Kwankwaso Ya Samu Karbuwa, an Fadi Damarsu a Zaben 2027

Tikitin Obi da Kwankwaso Ya Samu Karbuwa, an Fadi Damarsu a Zaben 2027

  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana ra'ayinsa kan tikitin da zai iya lashe zaben shugaban kasa a 2027
  • Babachir ya ce haɗakar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a takarar shugaban ƙasa za ta fi samun damar lashe zaɓen 2027 idan aka kwatanta da kowannensu ya tsaya shi kaɗai
  • Ya yi hasashen cewa haɗakar Obi da Kwankwaso za ta samu kashi 70 cikin 100 na damar yin nasara, yayin da Shugaba Bola Tinubu zai samu kashi 50 cikin 100

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya yi magana kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara.

Babachir Lawal ce Peter Obi da Rabiu Kwankwaso za su fi samun damar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 idan suka haɗa kai a takara maimakon kowannensu ya tsaya shi kaɗai.

Kara karanta wannan

Bayan zarginsa da shirin tsige Obasanjo, Atiku ya mayar da zazzafan martani

Babachir ya yi magana kan Obi da Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi a wajen taron NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Symfoni TV da aka wallafa ranar Asabar, 25 ga watan Yulin 2026.

Me Babachir ya ce kan Obi, Kwankwaso?

Babachir ya ce haɗakar Obi da Kwankwaso za ta samu kusan kashi 70 cikin 100 na damar yin nasara a zaɓen, yayin da ya ba Shugaba Bola Tinubu kashi 50 cikin 100 na damar lashe zaɓen.

Ya kuma yi hasashen cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ba zai samu nasara ba a zaben 2027.

Babachir Lawal ya kwatanta ‘yan takarar

Da yake magana kan yiwuwar haɗakar Peter Obi da Kwankwaso, Babachir Lawal ya bayyana cewa:

“Peter Obi zai yi ƙoƙarin yin adalci ga kowa. Peter Obi zai yi ƙoƙarin yin abin da ya dace. Peter Obi, Kwankwaso, ku lura, ina haɗa su ne. Ina haɗa su. Idan kowannensu ya tsaya shi kaɗai, abin ba zai yi kyau ba, amma ina haɗa su.”

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kashe N500m a kare martabar Najeriya kan zargin gallazawa kiristoci

“Saboda haka, a ma’aunina, zan ba su kusan kashi 70 cikin 100. Haka kuma Bola, kashi 50. Atiku, sifili."

Babachir Lawal ya ce Atiku zai sha kaye

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya ƙara da cewa Atiku ba zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.

“Tabbas, Atiku zai sha kaye. Zai sha kaye, kuma ina addu’ar ya sha kaye. Ba ni kaɗai ba ne, kuma zai sha kaye,” in ji shi.
Babachir Lawal ya yi hasashe kan zaben 2027
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal Hoto: Babachir David Lawal
Source: Twitter

Rikicin Babachir Lawal da Atiku

Kalaman Lawal sun zo ne bayan rashin jituwarsa da Atiku, sakamakon murabus ɗinsa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Tsohon SGF ɗin ya sha zargin cewa zaɓen fidda gwani na ADC da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ya cika da kura-kurai masu yawa, zargin da jam’iyyar ba ta amince da shi a hukumance ba.

Peter Obi ya gana da jakadan Birtaniya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Dan takarar jam'iyyar NDC a zaben shugaban kasa na 2027, Peter Obi, ya gana da babban jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery.

Peter Obi ya bayyana cewa sun tattauna kan dimokuradiyyar Najeriya, tattalin arziki da muhimmancin karfafa hukumomi gabanin zabuka masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng