Dalilin da Ya Sanya Buhari bai Goyi bayan Takarar Tinubu a Zaben 2023 ba

Dalilin da Ya Sanya Buhari bai Goyi bayan Takarar Tinubu a Zaben 2023 ba

  • Babachir Lawal ya ce Muhammadu Buhari bai mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaben fitar da gwani na APC ba saboda wasu dalilai
  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya ce ya shawo kan Buhari ya kasance tsaka-tsaki domin wakilan jam'iyya su zabi dan takara
  • Babachir sLawal ya yi ikirarin cewa Buhari ya yi hasashen Tinubu zai samu tikitin APC idan aka bar shi ya fafata ba tare da tsoma baki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya tuno abubuwan da suka faru a zaben fitar da gwani na jam'iyyyar APC a zaben 2023.

Babachir Lawal ya bayyana cewa marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, bai fito fili ya mara wa Bola Tinubu baya a zaben fitar da gwanin ba saboda wasu dalilai da suka shafi addini da kuma dabi'unsa.

Kara karanta wannan

'Yabon Trump ya nuna aikinmu ya na kyau': Fadar shugaban kasa

Babachir Lawal ya ce Buhari bai fito fili ya goyi bayan Tinubu a zaben 2023 ba
Shugaba Muhammadu Buhari yana daga hannun Bola Ahmed Tinubu a yakin neman zaben 2023. Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

Buhari bai goyi bayan Tinubu a 2023 ba

Lawal ya yi wannan bayani ne a wata hira da tashar Symfoni TV, inda ya ce Buhari da farko bai gamsu da cewa Tinubu ne ya dace ya gaje shi a matsayin shugaban kasa ba.

Sai dai bayan tattaunawa mai zurfi da suka yi, Buhari ya amince ya kasance tsaka-tsaki, ya kuma bar wakilan jam'iyyar su yanke hukuncin wanda zai zama dan takarar shugaban kasa.

A cewar Lawal, Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen yakin neman zaben Buhari a baya, inda ya samar da kudi da kuma kwararrun masu tsara yakin neman zabe.

Ya ce wannan gudunmawa ta sa Buhari ya ga ba zai dace ya hana Tinubu neman tikitin shugaban kasa kai tsaye ba.

Lawal ya kara da cewa ya tunatar da Buhari irin gudunmawar da Tinubu ya bayar wajen kafa APC da kuma nasarorin da jam'iyyar ta samu a zabukan baya.

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi

Yadda Babachir ya shawo kan Buhari

Lawal ya ce kafin taron fidda gwani na APC, ya ba Buhari shawarar kada ya mara wa kowane dan takara baya.

Ya ce ya bayyana wa shugaban cewa idan wakilan jam'iyyar suka ki zaben Tinubu, hakan zai kasance ba tare da sa hannunsa ba. A cewarsa, hakan ne ya fi dacewa domin kare martabar shugaban da kuma tabbatar da adalci a cikin jam'iyyar.

Sai dai ya ce Buhari ya nuna masa cewa idan aka bar shi ya jagoranci tsarin, Tinubu zai samu tikitin APC.

Buhari ya hango nasarar Tinubu

Lawal ya ce Buhari ya gaya masa cewa ya san salon siyasarsa tun daga shekarar 2002, kuma ya yi imanin cewa idan aka ba shi dama, zai tabbatar Tinubu ya zama dan takarar APC.

Babachir Lawal ya ce akwai dalilan da suka sanya Buhari bai goyi bayan Tinubu a 2023 ba
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa Abuja. Hoto: @MBuhari
Source: Facebook

Duk da haka, Lawal ya ce ya tabbatar wa Buhari cewa ko da Tinubu ya samu tikitin APC, har yanzu al'ummar Najeriya ne za su yanke hukunci a babban zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

'Mun daina bautawa siyasa', Fahad Dankabo ya kawo sabon salo a siyasar Kano

A karshe, Tinubu ya lashe zaben fidda gwani na APC bayan ya doke manyan abokan takararsa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, Ahmad Lawan da Yahaya Bello.

Daga bisani ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2023, inda aka rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya a ranar 29 ga Mayun 2023.

Kalli bidiyon a kasa:

Babachir ya fadi damar Obi a 2027

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana ra'ayinsa kan tikitin da zai iya lashe zaben shugaban kasa a 2027.

Babachir ya ce haɗakar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a takarar shugaban ƙasa za ta fi samun damar lashe zaɓen 2027 idan aka kwatanta da kowannensu ya tsaya shi kaɗai.

Ya yi hasashen cewa haɗakar Obi da Kwankwaso za ta samu kashi 70 cikin 100 na damar yin nasara, yayin da Shugaba Bola Tinubu zai samu kashi 50 cikin 100.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com