'Matsalar Tsaro Ta Zo Karshe," Tinubu Ya Bayyana Nasorin Gwamnatinsa a Shekaru 3
- Tinubu ya ce gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a fannonin tsaro, ilimi, ababen more rayuwa da tattalin arziki domin gina Najeriya mai ɗorewa
- Shugaban ƙasar ya bayyana cewa fiye da ɗalibai miliyan ɗaya sun amfana da shirin bashin karatu na NELFUND, yayin da aka inganta manyan cibiyoyin ilimi
- Ya kuma ce ana ci gaba da manyan ayyukan hanyoyi, layukan dogo da wutar lantarki domin bunƙasa tattalin arziki da haɗa sassan ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta inganta tsaro, ilimi, ababen more rayuwa da tattalin arziki, yana mai cewa sauye-sauyen da ake aiwatarwa za su samar da tubalin gina Najeriya mai ci gaba da wadata.
Tinubu ya bayyana haka ne ranar Asabar yayin taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina karo na uku da aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna.

Source: Twitter
Tinubu ya yi magana kan matsalar tsaro
Shugaban ƙasar, wanda mai tallafa masa na Musamman kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Masari ya wakilta, ya ce gwamnatinsa na ci gaba da kare manufofi da kyawawan ayyukan magabatan ƙasar ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen da za su amfani al'umma, in ji rahoton Vanguard.
Da yake magana kan tsaro, Tinubu ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa matsalolin rashin tsaro, musamman a Arewacin Najeriya, za su zo ƙarshe nan ba da jimawa ba.
Ya ce gwamnati na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
"Yayin da muke ci gaba da aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da tsaron ƙasarmu, da yardar Allah matsalolin rashin tsaro da ke addabar mu, musamman a Arewacin Najeriya, za su zama tarihi nan gaba kaɗan."
Daaliban da suka amfana da NELFUND
Game da harkar ilimi kuwa, shugaban ya ce gwamnatin tarayya ta faɗaɗa damar samun ilimin gaba da sakandare ta hanyar shirin bashin karatu na NELFUND, inda ya ce fiye da ɗalibai miliyan ɗaya suka riga suka ci gajiyarsa.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta dawo da kwanciyar hankali a manyan makarantun gaba da sakandare bayan cire su daga tsarin IPPIS tare da dakatar da cire kuɗaɗen shiga na cikin gida da suke samu.
A cewarsa, TETFund na ci gaba da gina dakunan karatu, dakunan kwanan ɗalibai, cibiyoyin bincike da na kimiyya, yayin da aka amince da sabon tsarin karatu na ƙasa tare da ƙarfafa ilimin sana'o'i da fasaha.
Tinubu ya kuma bayyana cewa an kafa sabbin jami'o'i da kwalejojin fasaha na gwamnatin tarayya a jihohi daban-daban domin ƙara wa matasa damar samun ingantaccen ilimi.
Ayyukan hanyoyi, layukan dogo da wutar lantarki
Shugaban ya ce ana ci gaba da aikin sake gina titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano da kuma aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry, in ji rahoton Punch.
Ya ce haka kuma ana gudanar da ayyukan titin Sokoto-Zamfara-Kaduna da kuma titin kilomita 434 daga Akwanga zuwa Jos, Bauchi da Gombe domin ƙarfafa haɗin kai da bunƙasa harkokin kasuwanci.
A bangaren makamashi, Tinubu ya ce gwamnatin tarayya na aiwatar da muhimman ayyukan inganta samar da wutar lantarki a Arewacin Najeriya, ciki har da tashar wutar Kaduna, aikin Kumbotso mai ƙarfin megawatt 40, cibiyoyin samar da hasken rana a karkara da kuma farfaɗo da tashar wutar Kaduna mai ƙarfin megawatt 215.
Ya kuma bayyana cewa an ɗaga Kwalejin Nazarin Man Fetur da Makamashi ta Kaduna zuwa jami'a, wadda aka sanya wa sunan marigayi Janar Hassan Usman Katsina.
Tinubu ya ƙara da cewa aikin tashar wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 1,350 a Gwagwalada na tafiya yadda ya kamata, yayin da ake aiwatar da wasu ayyukan makamashin sabuntawa a Kaduna da jihohin da ke makwabtaka.

Source: UGC
Gwamnati na faɗaɗa ayyukan sufuri da noma
Shugaban ya ce ana ci gaba da aikin layin dogo na Kaduna zuwa Kano da kuma Kano zuwa Maradi, yayin da gwamnatin tarayya ta ware kuɗaɗe domin ayyukan layukan dogo na cikin biranen Kaduna da Kano.
Ya ce ana kuma gyaran layin dogon Abuja Metro tare da shirin inganta zirga-zirgar jirgin ƙasa tsakanin Abuja da Kaduna domin sauƙaƙa jigilar fasinjoji da kayayyaki.
Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta samu ci gaba a fannonin noma, samar da abinci, tallafa wa matasa da shirye-shiryen jin ƙai.
A ƙarshe, ya yi kira ga 'yan Najeriya su ci gaba da haɗin kai tare da mara wa gwamnati baya domin gina ƙasa mai zaman lafiya da ci gaba.
Gwamna Sule ya yabawa Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce Shugaba Bola Tinubu ya fi sauran masu neman takarar shugaban ƙasa.
Abdullahi Sule ya ce banbancin da ke tsakanin Tinubu da abokan hamayyarsa ya yi kama da dare da rana.
Gwamnan ya bayyana ayyukan raya ƙasa, ilimi da ci gaban kasuwar hannayen jari a matsayin nasarorin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng