Shekaru 3 a kan Mulki: An Jero Manyan Ayyukan da Tinubu Zai Kaddamar a Abuja
- Nyesom Wike ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai fara kaddamar da manyan ayyukan tituna da more rayuwa a Abuja daga ranar Talata
- Ministan Abujan ya ce an kammala wasu manyan ayyuka 100 bisa 100 yayin da Tinubu zai ziyarci wasu yankunan karkarar babban birnin
- Wike ya yabawa Tinubu kan goyon bayan da ya bai wa gwamnatin Abuja wajen kammala ayyukan da suka dade ana jiran a yi su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai fara kaddamar da wasu manyan ayyukan more rayuwa a Abuja daga ranar Talata.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai domin duba yadda aka kammala shirye-shiryen kaddamar da ayyukan a ranar Litinin.

Source: Twitter
Bola Tinubu zai kaddamar da ayyuka a Abuja
Ministan ya ce shugaban kasar zai fara da kaddamar da mataki na biyu na babban titin Outer Southern Expressway (OSEX), wanda ya bayyana cewa an kammala shi 100 bisa 100, in ji rahoton Tribune.
Wike ya nuna farin cikinsa kan yadda aka samu nasarar kammala manyan ayyukan cikin kankanin lokaci a sassa daban-daban na Abuja.
Ya ce:
“Gobe (Talata) shugaban kasa zai fara kaddamar da titin OSEX wanda shi ne wurin farko da muka ziyarta da safiyar yau.”
Jerin ayyukan da za a kaddamar
Ministan ya kara da cewa shirin kaddamar da ayyukan zai ci gaba na kwanaki domin murnar cika shekaru uku na gwamnatin Tinubu.
A cewarsa, a ranar Laraba shugaban kasa zai kaddamar da titin Arterial Road N5 da ke Life Camp.
Haka kuma ranar Alhamis zai kaddamar da sabon titin Highway 105 wanda aka fadada daga filin jirgin sama zuwa Kuje domin inganta zirga-zirga da bunkasa tattalin arziki.
“An kammala wadannan ayyuka uku 100 bisa 100 kuma an shirya komai domin kaddamar da su. Abu mafi muhimmanci shi ne mun cika wa’adin da muka dauka,” in ji Wike.
Tinubu zai ziyarci yankunan karkara
Wike ya kuma bayyana cewa shugaban kasa zai kai ziyara yankunan karkara na Abuja domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da aka yi a kananan hukumomi.
Sai dai ya ce ba zai bayyana cikakken jerin wuraren da shugaban kasar zai ziyarta ba a yanzu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Source: Facebook
Ministan ya gode wa shugaban kasa bisa goyon bayan da yake bai wa Gwamnatin Abuja wanda ya ba su damar cimma wadannan nasarori.
Da aka tambaye shi game da sababbin tashoshin mota da aka kammala amma ba a fara amfani da su ba, Wike ya bukaci mazauna Abuja su kara hakuri.
Ya bayyana cewa Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da tsarin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin gudanar da tashoshin.
Wike ya jero ayyukan alherin Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yabi shugaban kasa, Bola Tinubu bisa ayyukan alherin da yake wa al'umma tun da ya hau mulki.

Kara karanta wannan
"Ku daina yi wa Fulani kudin goro," Peter Obi ya yi jan hankali kan ayyukan 'yan bindiga
Wike ya bayyana cewa makaho ne kaɗai zai ce Shugaba Tinubu ba ya aiki a Abuja amma an samu canji tun daga 29 ga watan Mayu, 2023 da ya karbi ragamar kasar.
Tsohon gwamnan ya ce yana fatan za a kaddamar da ayyuka da dama a bikin cikar Shugaban kasa, Bola Tinubu shekaru biyu a kan mulki.
Asali: Legit.ng

