World Cup 2026: Jerin Kasashe 4 da Za Su Halarci Gasar Cin Kofin Duniya a Karon Farko
Yayin da ya rage saura awanni kadan a fara gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026, masu sha'awar kwallon kafa a fadin duniya na ci gaba da nuna farin ciki da shirin fara babbar gasar kwallon kafa mafi girma a duniya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Za a gudanar da gasar bana ne a kasashen Amurka, Mexico da Canada kuma za a buga wasan farko na bude wannan gasa a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, 2026.

Source: Getty Images
Rahoton ESPN ya nuna cewa gasar ta 2026 za ta kasance ta musamman domin a karon farko za a kara yawan kasashen da za su halarta daga 32 zuwa 48.
Wannan lamarin da ya bai wa karin kasashe damar shiga gasar ciki har da wadandaba su taba taka leda a gasar kofin duniya ba a tarihi.
A Kofin Duniya na 2022 da aka yi a Qatar, kasa mai masaukin baki ce kadai ta fara halartar gasar ta kwallon kafa a karon farko.
Sabon shiga Gasar cin kofin kwallon duniya
Sai dai fadada gasar ya bai wa kasashe hudu damar bayyana a kofin duniya karo na farko a tarihinsu a wannan shekara ta 2026. Ga su kamar haka:
1. Kasar Cape Verde
Cape Verde ta kafa tarihi a matsayin daya daga cikin kananan kasashe mafi karancin yawan jama'a da suka taba kai wa gasar kofin duniya.
Kasar tsibiri ce da ke gabar yammacin Afirka, kuma ta samu tikitin shiga gasar bayan taka rawar gani a wasannin neman gurbin shiga.
Tawagar da ake wa lakabi da Blue Sharks ta samu nasarori masu muhimmanci kan Angola da Kamaru a hanyarta ta zuwa gasar, kamar yadda tashar Al-jazeera ta ruwaito.

Source: Getty Images
Duk da cewa wannan ne karon farko da za ta buga Kofin Duniya, Cape Verde ta taba halartar gasar AFCON sau hudu.
Mafi kyawun bajintarta ita ce kai wa zagayen kwata fainal a AFCON 2023 kafin Afirka ta Kudu ta fitar da ita a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Kara karanta wannan
Bayan Tinubu ya rantsar da shi, sabon ministan lantarki ya fara da bai wa yan Najeriya hakuri
Tawagar za ta fara gasar ne da Spain kafin ta kara da Uruguay da Saudi Arabia a rukuni na H.
2. Kasar Curaçao
Tashar NBC News ta wallafa rahoton cewa Curaçao ta kafa tarihi a matsayin kasa mafi karancin yawan jama'a da ta taba samun tikitin shiga gasar kofin Dduniya.
Kasar da ke yankin Caribbean mai alaka da Netherlands na da yawan jama'a kusan 150,000 kacal.
Tawagar ta samu gurbin shiga gasar ne ba tare da shan kashi ko daya ba, inda ta yi nasara a wasanni bakwai tare da canjaras uku.

Source: Facebook
Babban kocin kungiyar, Advocaat, mai shekara 78, na dab da zama mafi tsufa cikin masu horar da kungiyoyi a tarihin Kofin Duniya. Curaçao za ta fafata da Jamus, Ecuador da Côte d’Ivoire a rukuni na E.
3. Kasar Jordan
Jordan ta dade tana kokarin samun gurbin shiga Kofin Duniya, amma ba ta yi nasara ba, inda kasar ta kusa cimma burinta a shekarar 2014, amma Uruguay ta hana ta zuwa a wasan neman gurbi.

Kara karanta wannan
Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya
Yanzu dai bayan shekaru masu yawa, Jordan ta samu damar taka leda a Kofin Duniya karo na farko, kamar yadda BBC News ta rahoto.
Nasarar da ta samu a gasar cin kofin Asiya ta 2023, inda ta kai wasan karshe, ta nuna irin ci gaban da kwallon kafar kasar ke samu.

Source: Getty Images
A karkashin jagorancin koci Jamal Sellami, Jordan ta yi fice a wasannin neman gurbi inda ta lashe wasanni takwas tare da shan kashi uku kacal.
Jordan za ta kara da Austria, Algeria da kuma zakaran kofin duniya mai ci Argentina a rukuni na J.
4. Kasar Uzbekistan
Rahoton Fox Sport ya nuna cewa Uzbekistan ta zama kasa ta farko daga yankin Asiya ta Tsakiya da ta taba samun gurbin shiga Kofin Duniya.
Kasar ta dade tana kokarin cimma wannan buri, amma a bana ta yi nasarar kafa tarihi, inda tawagar yan wasanta ta yi fice a wasannin neman gurbi, ta sha kashi sau daya kacal.
Abin da ya kara daukar hankali shi ne kasancewar tsohon kyaftin din Italiya kuma gwarzon kofin duniya, Fabio Cannavaro, a matsayin kocin tawagar yan wasan Uzbekistan.

Kara karanta wannan
"Ku daina yi wa Fulani kudin goro," Peter Obi ya yi jan hankali kan ayyukan 'yan bindiga

Source: Getty Images
Kyaftin din kungiyar, Eldor Shomurodov, ne ke jagorantar tawagar, yayin da dan wasan baya na Manchester City, Abdukodir Khusanov, ke cikin taurarin da ake sa ran za su haskaka a gasar.
Uzbekistan za ta fara gasar ne da Colombia kafin ta kara da Portugal da DR Congo a rukuni na K.
Iran za ta halarci gasar Kofin Duniya
A wani rahoton, kun ji cewa an bai wa tawagar ƙwallon ƙafar Iran bizar shiga Amurka gabanin gasar kofin duniya da za a fara a watan Yunin 2027.
Tun a kwanakin baya aka yi ta takaddama kan ko 'yan wasan kasar musulunci za su taka leda a Amurka lura da yakin da ya barke da Iran a Gabas ta Tsakiya.
Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya nuna cewa gwamnatin Trump ba ta da wata matsala wajen bayar da bizar ga tawagar Iran
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
