Majalisa na So Tinubu Ya Hana 'Yan Najeriya Shigo da Tufafi daga Kasashen Waje
- Majalisar Dattawa ta nemi a hana shigo da tufafi daga waje domin farfado da masana’antar masaku tare da samar da ayyukan yi a Najeriya
- Sanatoci sun bukaci gwamnati ta karfafa noman auduga domin bunkasa masana’antar tufafi da rage matsalar rashin aikin yi a kasar
- Majalisar ta bukaci Kwastam ta tsaurara tsaro a iyakoki domin dakile fasa-kwaurin tufafi da kayayyakin masaku zuwa Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da shigo da dukkan nau’ukan tufafi daga kasashen waje domin farfado da masana’antar tufafi ta kasar da ta dade tana durkushewa.
Majalisar ta kuma bukaci hukumar Kwastam ta Najeriya da ta kara tsaurara tsaro a dukkan iyakokin kasar domin dakile ayyukan fasa-kwauri da ke taimakawa shigowar wadannan kayayyaki.

Source: Getty Images
Matsalar masana'antar tufafi ta Najeriya
Haka kuma ‘yan majalisar sun yi kira ga gwamnati da ta ba da muhimmanci ga noman auduga, kasancewar shi ne muhimmin sinadari da ake bukata wajen farfado da masana’antar, in ji rahoton NAN.
Wannan batu ya biyo bayan wani kudurin doka da Sanata Sunday Marshall Katung (Kaduna ta Kudu) ya gabatar tare da wasu sanatoci tara.
Sanata Katung ya tunatar da cewa masana’antar tufafi ta Najeriya ta fara samun gindin zama ne tun shekarar 1957 a Kaduna, wanda hakan ya haifar da bunkasar masana’antar a sassa daban-daban na kasar.
Sai dai ya koka kan yadda masana’antar ta rika durkushewa sakamakon rashin ingantattun kayan aiki, karancin zuba jari da kuma rashin daidaiton manufofin gwamnati.
“Zuwa 1997, yawancin wadannan kamfanoni sun fara durkushewa saboda tsofaffin injina da rashin wutar lantarki mai dorewa. Zuwa 2007 kuma, mafi yawansu sun rufe gaba daya, abin da ya janyo asarar ayyukan yi sama da 70,000,” in ji Katung.
Neman farfado da masana’antar tufafin Najeriya
Sanata Mohammed Monguno ya bayyana cewa masana’antar masaku ta Najeriya wadda a da take da matukar muhimmanci ta durkushe sakamakon shigo da kaya daga waje da kuma tsadar samarwa a cikin gida.
Ya bukaci a kafa asusun tallafi na musamman daga Babban Bankin Najeriya domin farfado da masana’antar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A nata bangaren, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jaddada muhimmancin noman auduga, tana mai cewa shi ne tushen duk wani cigaba a masana’antar masaku.
Ta bayar da misali da kasashe irin su Amurka da Habasha da suka samu ci gaba ta hanyar amfani da auduga wajen bunkasa tattalin arziki.

Source: Twitter
Matakin da Majalisar dattawa ta dauka
Sanata Adams Oshiomhole ya dora laifi kan manufofin kasuwanci da ya ce ba su dace ba, wadanda suka taimaka wajen rushewar masana’antar.
Ya bukaci Majalisar Dattawa ta tabbatar da cewa wannan kudiri ba zai fuskanci makomar sauran kudurorin da suka gabata ba.

Kara karanta wannan
Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya
Bayan haka, majalisar ta kuma bukaci ma’aikatar noma da ma’aikatar kasuwanci da masana’antu su hada kai wajen farfado da masana’antar tufafi a fadin kasar.
A cewar ‘yan majalisar, farfado da masana’antar masaku zai samar da ayyukan yi, rage tashin hankalin matasa da kuma inganta tsaro a Najeriya.
Shirin farfado da masakar Kaduna
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin tarayya za ta farfado da kamfanin auduga na Kaduna domin bunkasa masana’antu da tattalin arzikin Najeriya.
Sanata George Akume ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na aiki tukuru a fannoni takwas don ganin an samu ci gaba a ƙasar.
A baya dai hukumar haraji ta Kaduna ta rufe kamfanin sarrafa auduga na UNTL saboda bashin haraji da ya kai Naira biliyan 1.2
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

