Rasha, China Sun Yi Magana bayan Iran da Amurka Sun Sake Fara Gwabza Yaki

Rasha, China Sun Yi Magana bayan Iran da Amurka Sun Sake Fara Gwabza Yaki

  • Kasar Rasha ta bayyana matukar damuwa kan sabon rikici da ya barke tsakanin Amurka da Iran da ya kai ga kai hare-hare masu zafi
  • A wata sanarwa da ta fitar, Moscow ta bukaci bangarorin da su dakatar da hare-haren soji tare da komawa tattaunawa a teburin sulhu
  • A daya bangaren, kasar China ma ta nuna damuwa kan rikicin tare da kira ga bangarorin da su yi hakuri kuma su guji kara dagula lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Russia - Kasashen duniya sun fara magana kan sabon rikici da ya barke a Gabas ta Tsakiya tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kasashen Rasha da China masu fada a ji a duniya sun nuna damuwa game da sake kai hare-hare ga juna da Iran da Amurka suka yi.

Kara karanta wannan

Xenophobia: Najeriya da kasashe 4 da suka fara kwaso mutanensu daga Afrika ta Kudu

Valadimir Putin da Xi Jinping
Shugaba Vladimir Putin da Xi Jinping a kasar China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadin da kasar Rasha ta yi

Anadolu Agency ta rahoto cewa Rasha ta ce tana cikin matukar damuwa game da karuwar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya, tana kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi hakuri tare da dakatar da hare-haren da suke kai wa juna nan take.

“Muna cikin matukar damuwa game da sabon zagayen rikicin makami tsakanin Amurka da Iran, wanda ya fara ne da harin da Amurka da Isra’ila suka kai ba tare da tsokana ba kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran,”

In ji mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha, Maria Zakharova, yayin wani taron manema labarai.

Ta yi kira ga bangarorin da su yi hakuri tare da dakatar da hare-haren soji nan take, Zakharova ta jaddada cewa kai hari kan cibiyoyin fararen hula abu ne da ba za a amince da shi ba ko kadan.

Zakharova ta ce Rasha har yanzu tana da yakinin cewa babu wata mafita ga rikicin face ta hanyar siyasa da diflomasiyya bisa dokokin kasa da kasa da kuma muradun tsaron dukkan kasashen yankin.

Kara karanta wannan

Sojojin Iran sun saki bama bamai kan Amurka bayan harin Trump a Tehran

“Muna fatan lamarin zai koma cikin tsarin siyasa da diflomasiyya da wuri-wuri,”

Mai magana da yawun Moscow ta bayyana cewa a wannan bangare, Rasha a shirye take ta taimaka wajen ganowa da kuma aiwatar da hanyoyin warware rikicin da dukkan bangarori za su amince da su.

Harin da Iran ta kai Bahrain
Wajen da Iran ta kai farmaki Bahrain bayan harin da Amurka ta kai mata. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kasar China ta yi gargadi

A nata bangaren, China ta ce tana cikin matukar damuwa game da rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, tare da kira da a guji kara ruruta rikicin bayan Washington ta kai hare-hare kan Iran sakamakon harbo wani jirgin Amurka.

Rahoton Al-Arabiyya ya nuna cewa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Lin Jian ya ce:

“ Ya kamata dukkan bangarorin da abin ya shafa su kwantar da hankali tare da yin hakuri, su dakatar da kara tsananta rikicin da dagula lamarin,"

Amurka ta kai hari Kasar Iran

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojojin Amurka ta ce jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare wasu wurare a kasar Iran.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar Trump, Amurka ta kai hare hare kasar Iran

Ta ce hare-haren sun shafi tsarin kariyar sararin samaniya da cibiyoyin tsaro na Iran da ke kusa da mashigar ruwan Hormuz.

Shugaba Donald Trump ya sha alwashin cewa za su mayar da martani kan harbo jirgin Apache na rundunar sojin Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng