Sojoji Sun Shawo kan Masu Zanga Zanga da Suka Rufe Hanyar Zamfara, An Ji Raunuka

Sojoji Sun Shawo kan Masu Zanga Zanga da Suka Rufe Hanyar Zamfara, An Ji Raunuka

  • Sojoji sun samu damar kwantar da tarzoma bayan mazauna Zurmi sun gudanar da zanga-zanga kan matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin
  • Sojojin Brigade ta 1 sun kai dauki bayan masu zanga-zangar sun toshe hanyar Zurmi zuwa Dauran domin bayyana takaicin yadda ake garkuwa da su
  • Mazauna yankin na daga cikin mutanen da ke zama a cikin fargaba saboda yawaitar harin masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Sojojin Brigade ta 1 sun dawo da zaman lafiya a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara bayan an yi zanga-zanga.

Mazauna yankin sun yi tururuwa zuwa tituna tare da rufe hanya saboda matsalar tsaro da ke kara kamari da tayar da hankula.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 6 sun mutu yayin da suka yi yunkurin kai hari a jihar Zamfara

Dakarun tsaro ta aika sojoji zuwa jihar Zamfara
Wasu daga cikin dakarun sojin Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Jaridar Zagazola Makama ta wallafa cewa majiyoyin tsaro sun tabbatar mata da yadda suka yi nasarar kwantar da tarzoma bayan an yi zanga-zanga.

Sojoji sun kwantar da tarzoma a Zamfara

Rahoton ya bayyana cewa dakarun sun isa wurin da 8:45 na safiyar ranar 8 ga Yuni, 2026 bayan samun bayanan cewa fararen hula sun fito zanga-zanga tare da toshe hanyar Zurmi zuwa Dauran.

An ce masu zanga-zangar sun nuna damuwarsu kan matsalolin tsaro da ke shafar al'ummomi da dama a fadin karamar hukumar, lamarin da ya hana zirga-zirgar ababen hawa a wannan muhimmiyar hanya.

A cewar majiyoyin tsaro, an tura karin dakaru zuwa wurin domin hana rikici barkewa tare da tabbatar da cewa zirga-zirga ta ci gaba kamar yadda aka saba.

Dakarun sun yi nasarar tarwatsa masu zanga-zangar tare da sake bude hanyar da aka rufe, wanda hakan ya bai wa jama'a damar ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a wasu garuruwan Sokoto, an gwabza da sulhu ya rushe

Wasu sojoji sun ji rauni a jihar Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa yayin gudanar da aikin, sojoji uku sun samu raunuka kadan, inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa sojojin da suka samu raunukan suna cikin koshin lafiya kuma suna ci gaba da samun kulawa.

Mutanen Zamfara sun yi zanga zanga a kan rashin tsaro
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Haka kuma, an bayyana cewa an riga an dawo da zaman lafiya a yankin, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki domin hana sake aukuwar wata matsala.

Mahukunta sun bukaci mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda tare da gabatar da koke-kokensu ta hanyoyin lumana da suka dace.

Sun kuma jaddada cewa ana ci gaba da kokarin magance matsalolin rashin tsaro da suka dade suna damun al'ummomin da ke yankin domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

'Yan sanda sun shiga dajin Zamfara

A baya, mun wallafa cewa dakarun rundunar yan sanda sun karbe iko da dajin Jangebe da ke jihar Zamfara bayan artabu da miyagun 'yan bindiga da suka nemi mafaka har da kai wa jama'ar gari hari.

Kara karanta wannan

Dakarun 'yan sanda sun kutsa dajin Zamfara, sun yi gaba da gaba da 'yan bindiga

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar, ya ce jami'an tsaron sun yi nasarar hallaka yan bindiga uku a musayar wuta, sannan sun fatattaki sauran da ke artabu da su a yayin arangamar.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da kai farmaki a maboyar ‘yan ta’adda domin dawo da zaman lafiya a Zamfara tare da ci gaba da kokarin wanzar da lafiya a sassan jihar da kewaye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng