Ana Neman Ruguza Kwankwaso a Kano, Barau Ya kai Hanga wajen Tinubu
- Sanata Rufai Hanga mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya jagoranci Hanga da tsohon Sanata Kabiru Gaya zuwa ganawar da suka yi da Tinubu
- Ganawar ta zo ne yayin da ake ta raɗe-raɗin cewa Sanata Rufai Hanga na shirin ficewa daga jam'iyyar NDC zuwa APC bayan tuntuba da ya ke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Rufai Hanga, ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Lamarin da ya ƙara rura wutar jita-jitar cewa yana shirin komawa jam'iyyar APC mai mulki tare da raba hanya da Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Facebook
Rahoto ya nuna cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ne ya bayyana hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi.
Barau ya kai Hanga wajen Tinubu
A cewar Barau, shi ne ya jagoranci Sanata Rufai Hanga da tsohon Sanata Kabiru Gaya zuwa fadar shugaban ƙasa domin ganawa da shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunar sojojin Najeriya.
Barau ya rubuta cewa:
"A ɗan lokaci da ya wuce, na samu damar jagorantar Sanata Rufai Hanga mai wakiltar Kano ta Tsakiya da tsohon Sanata Kabiru Gaya zuwa fadar shugaban ƙasa domin ganawa da shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunar sojojin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu."
Jita-jitar komawar Hanga APC ta ƙaru
Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yaɗa jita-jitar cewa Sanata Rufai Hanga na shirin sauya sheƙa zuwa APC bayan wasu ganawa da yake yi da manyan jiga-jigan jam'iyyar.
A wani sako da ya wallafa a Facebook a ranar Lahadi, 26 ga Yuli, 2026, Sanata Hanga ya ce ya gana da masu kula da mazabunsa daga ƙananan hukumomi 15 na Kano ta Tsakiya.
A yayin taron, ya yi musu bayani kan halin da siyasar tawagarsa ke ciki tare da neman shawararsu kan makomar siyasarsa, musamman batun yiwuwar komawa wata jam'iyya.

Source: Twitter
Majiyoyi masu tushe sun shaida cewa waɗannan ganawa na daga cikin shawarwarin da ake yi dangane da yiwuwar komawar Hanga daga jam'iyyar NDC zuwa APC.
Rahoton ya kuma tuna cewa Hanga na daga cikin fitattun 'yan siyasar da suka ci gaba da kasancewa tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC.
An soki Ganduje kan Kwankwaso/Obi
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar NDC da ƙungiyar Obedient Movement sun mayar da martani ga tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, kan kalamansa game da haɗakar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
Ganduje ya bayyana cewa tikitin takarar shugaban ƙasa na Obi da Kwankwaso a ƙarƙashin NDC ba zai yi tasiri ba a Kano, yana mai cewa ba su da ƙarfin da za su iya lashe zaɓen 2027.
Sai dai mataimakin sakataren yaɗa labarai na NDC na ƙasa, Abdulmumin Abdulsalam, ya yi watsi da wannan ikirari, yana mai cewa Ganduje ba shi da matsayin da zai iya tantance makomar siyasar haɗakar.
Asali: Legit.ng

