Lamari Ya Rikice: Sheikh Assadus Sunnah Ya Janye daga Shiga Sabgar Yan Bindiga

Lamari Ya Rikice: Sheikh Assadus Sunnah Ya Janye daga Shiga Sabgar Yan Bindiga

  • Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya ce ya daina shiga harkokin sasanta 'yan bindiga, yana mai cewa ya yi iya ƙoƙarinsa
  • Malamin ya koka cewa lokacin da suke neman mafita ga matsalar tsaro, wasu suna zarginsu da goyon bayan ta'addanci
  • Ya ƙalubalanci masu zarginsu da karɓar kuɗi su fito da hujja, yana cewa babu wanda ya amfana da aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Babban malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya yi maganganu kan ta'addanci a Najeriya.

Malamin ya nuna damuwa game da yadda aka rika sukarsu lokacin da suka yi ta kokarin ganin an samu sauki a hare-haren da ake yi a Arewa.

Assadus Sunnah ya janye daga shiga lamarin yan bindiga
Babban malami da ke shiga daji saboda yan bindiga, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah. Hoto: Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah.
Source: Facebook

Wakilin Legit Hausa ne ya bibiyi wani bayani da malamin ya yi a wani faifan bidiyo wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Minista ya yi barazanar hada yan kwangila da EFCC, ya ba su wa'adin awa 72

Malami ya janye jikinsa daga lamarin yan bindiga

A cikin bidiyon, malamin ya ce babu ruwansa yanzu da shiga lamarin yan bindiga kamar yadda ya yi a baya.

Ya ce abin takaici ne lokacin da suke kokarin ganin an samu sauki a hare-hare amma mutane suna yi masu kallon suna samun wani abu.

Ya ce:

"Maganar tsaro kuwa, babu ruwanmu yanzu, kowa ya yi ta kansa, abin da za mu iya yi a baya sanda muke da dama mun yi.
"Masu surutu da yan fashe-fashen baki da yan wace tsiya a yanzu duk wanda ya san wani abu yanzu ya fito ya yi, mu dai mun tsaya iya nan.
"Saboda haka maganar ni in sake zuwa daji da sunan wani alkawari, a'a wadanda suka ce mu munafukai ne a baya, cewa muna goyon bayan barna, to mun bari."
Malami ya fusata kan yadda aka yi ta sukara game da yan bindiga
Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah da daya daga cikin jagororin yan bindiga, Ado Aliero. Hoto: Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah, HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Shawarar da malamin ya ba mutane

Sheikh Assadus Sunnah ya bukaci duk mai sha'awar kawo sauyi a lamarin tsaro zai iya shiga yanzu domin ba da tashi gudunmawa.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya kare kansa da aka tsoma shi a matsalar sace dalibai a Oyo

"Idan da wani da zai yi abin da muka yi a baya, to sai ya tashi ya yi, ni ban kara zuwa koina, ko da muke aikin nan fa, ko albashi ba mu da shi.
"Na rantse da girman Allah ko albashi ba wanda ya ke ba mu, amma haka wani dan iska yana zaune yana kallon muna goyon bayan barna, wani kuma gani ya ke yi wata duniya kake samu."

- Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah

Malamin ya kalubalanci mutane idan akwai wanda ya taba ba su kudi to ya fito ya fadi abin da ya basu, ya ce har suka gama a cikinsu babu wanda ko mota ya saya.

Shugaban Izala ya rasu a hannun yan bindiga

An ji cewa rahotanni sun tabbatar da sanar da rasuwar Malam Yahaya Billi, Shugaban Izala na Besse, bayan ya rasu a hannun yan bindiga.

Marigayin yana daga cikin wadanda yan bindiga suka ce a jihar tare da wani tsohon shugaban APC a wani yankin jihar Kebbi.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana'izarsa ta Ga'ib wanda aka yi a Garkan Sarki da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.