Nnamdi Kanu: Dan Majalisar Amurka Ya Yi wa Tinubu Barazana Mai Girma
- Wani dan majalisar dokokin Amurka John James ya bukaci gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu da ake tsare da shi
- James ya nemi a sake yi wa Kanu shari'a bisa kundin tsarin mulkin Najeriya da ka'idojin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa
- IPOB ta yaba da matakin dan majalisar Amurka, tana cewa hakan ya nuna ƙarin kulawar ƙasashen duniya kan shari'ar Nnamdi Kanu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Michigan, US - Dan majalisar wakilan Amurka mai wakiltar jihar Michigan, John James, ya yi barazana ga gwamnatin Bola Tinubu.
James ya bukaci gwamnatin Najeriya ta saki shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ko kuma ta fuskanci yiwuwar rage tallafin Amurka.

Source: Twitter
James ya bayyana wannan matsaya ne yayin zaman majalisar wakilan Amurka, inda ya nemi goyon bayan ƙudurin H.Res. 1321 da ya gabatar tun ranar 22 ga Mayun 2026, cewar TheCable.
Kanu: Bukatar dan majalisar Amurka ga Najeriya
Har ila yau, ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake yi wa Kanu shari'a bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma ka'idojin kare haƙƙin ɗan Adam na duniya.
Ƙudurin yana gaban kwamitin harkokin wajen majalisar, kuma ya bukaci gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa duk matakan shari'ar Kanu sun dace da kundin tsarin mulki.
Da yake jawabi a zaman majalisar, James ya yi zargin cewa shari'ar Kanu na daga cikin abin da ya kira tsananta wa Kiristoci a Najeriya.
Ya kuma yi zargin cewa dubban Kiristoci sun rasa rayukansu tun shekarar 2019 sakamakon hare-haren masu tsattsauran ra'ayi, yana cewa gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba.
James ya kuma yi ikirarin cewa kungiyoyi irin su Boko Haram sun ci gaba da gudanar da hare-hare ba tare da isasshen martani daga hukumomin Najeriya ba.

Source: Facebook
Dan majalisar Amurka ya yaba wa Kanu
Dan majalisar ya bayyana Kanu a matsayin mutum mai jajircewa, yana mai cewa an yanke masa hukunci ne bayan abin da ya kira shari'ar da ba ta cika ka'ida ba, cewar Vanguard.
Ya bukaci 'yan majalisar Amurka su goyi bayan ƙudurinsa domin a sake yi wa Kanu shari'a cikin adalci tare da ba shi damar samun lauyoyi, kulawar lafiya da kyakkyawan yanayin tsarewa.
James ya kuma ce ya kamata Amurka ta sake nazarin tallafin kuɗin da take bai wa Najeriya idan ba a saki Kanu ba.
A wata sanarwa, kakakin IPOB, Emma Powerful ya yaba da wannan mataki, yana cewa ya nuna ƙarin kulawar ƙasashen duniya kan batun sakin Kanu.
Kungiyar IPOB ta bayyana fatan cewa wannan kira zai ƙarfafa gwamnatin Najeriya ta sake duba shari'ar Kanu, wanda ke zaman gidan yari a Sokoto bayan hukuncin ɗaurin rai da rai kan laifukan ta'addanci.
Amurka za ta dakatar da tallafi ga Najeriya
A wani labarin, an ji cewa Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudirin dakatar da duk tallafin Amurka ga ƴan Najeriya da kasar baki daya.
Masana sun gargadi cewa idan kudirin ya zama doka, shirye-shiryen HIV, tarin fuka, zazzabin cizon sauro, rigakafi da lafiyar mata da yara za su shiga hadari.
Sun bukaci gwamnatin Najeriya ta inganta tsaro, karfafa dangantaka da Amurka, tare da samar da hanyoyin cikin gida domin daukar nauyin lafiya.
Asali: Legit.ng

