Za a Sheka Ruwan Sama na Kwanaki 3 a Kaduna da Jihohi 3 na Najeriya

Za a Sheka Ruwan Sama na Kwanaki 3 a Kaduna da Jihohi 3 na Najeriya

  • Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen yanayi mai cike da rana, gajimare da tsawa a sassa daban-daban na ƙasar daga Lahadi zuwa Talata
  • NiMet ta yi gargaɗin cewa iska mai ƙarfi na iya gabatar da ruwan sama a wuraren da ake sa ran samun tsawa
  • Hukumar NiMet ta shawarci jama’a da su guji tuki ko shiga ruwan ambaliya, tare da cire kayan lantarki daga soket

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

FCT, Abuja – Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun rana, gajimare da tsawa a sassa daban-daban na ƙasar daga Lahadi zuwa Talata.

A cikin hasashen yanayin da ta fitar a Abuja ranar Lahadi, NiMet ta ce za a samu sararin sama mai rana tare da ɗan gajimare a yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Trump ya lallaba ya tura bukatar tsagaita wuta Iran ta Iraq, Tehran ta yi martani

An yi hasashen ruwan sama
Wasu mutane na tafiya a cikin ruwan sama. (An yi amfanin da hoton ne don misali) Hoto: Getty Images
Source: UGC

Hukumar ta kuma yi hasashen tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan jihohin Taraba, Adamawa da Kaduna da safe, kamar yadda ta sanya a shafinta na X.

Da rana da kuma yamma, ana sa ran tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan jihohin Borno, Bauchi, Gombe, Jigawa, Katsina, Kano, Kaduna, Adamawa da Taraba.

A yankin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan jihohin Plateau, Neja, Nasarawa da Babban Birnin Tarayya (FCT) da safe.

Daga baya da rana ko yamma, ana sa ran tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan jihohin Kogi, Benue, Plateau, Neja da Nasarawa, da kuma FCT.

Hasashen yanayin kudancin Najeriya

A cewar hukumar, ana sa ran matsakaicin ruwan sama a wasu sassan jihohin Ondo, Ogun, Cross River, Akwa Ibom, Rivers, Lagos da Bayelsa da safe.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An gano jami'ar bogi da ta tara dalibai a Najeriya

NiMet ta ce ana sa ran matsakaicin ruwan sama a dukkan yankin Kudancin ƙasar daga baya da rana.

Hasashen yanayi na ranar Litinin

A ranar Litinin, NiMet ta yi hasashen tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Adamawa da Taraba a yankin Arewa da safe.

Daga baya a rana, hukumar ta yi hasashen tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan jihohin Borno, Jigawa, Yobe, Bauchi, Gombe, Kano, Katsina, Kaduna, Taraba da Adamawa.

A yankin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan jihohin Neja da Kwara, da kuma FCT da safe.

Daga baya da rana ko yamma, ana sa ran tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a fadin yankin.

A kudancin ƙasar, ana sa ran ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan jihohin Cross River, Delta, Bayelsa, Akwa Ibom, Lagos da Rivers da safe.

Hukumar ta ƙara da cewa ana sa ran tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a fadin yankin Kudancin ƙasar daga baya da rana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana bayan ganin kumfa a Kaduna

Hasashen yanayi na ranar Talata

A cewar NiMet, ana sa ran sararin sama mai ɗan gajimare a yankin Arewa ranar Talata, tare da yiwuwar samun tsawa da ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan jihohin Bauchi, Jigawa da Yobe da safe.

Hukumar ta yi hasashen tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a fadin yankin da rana da kuma yamma.

An yi hasashen yanayi na ruwan sama
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A yankin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran samun rana tare da ɗan gajimare da safe. Daga baya da rana ko yamma, ana sa ran tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a fadin yankin.

A kudancin ƙasar, ana sa ran yanayi mai cike da gajimare tare da yiwuwar samun ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan jihohin Edo, Cross River, Delta, Bayelsa, Akwa Ibom da Rivers da safe.

NiMet ta ce ana sa ran tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a fadin yankin kudancin ƙasar daga baya da rana.

NiMet ta yi hasashen yanayi

Kara karanta wannan

Kaduna da jihohin Najeriya 16 za su fuskanci ambaliyar ruwa a cikin kwanaki 7

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Najeriya, watau NiMet, ta fitar da hasashen yanayi.

NiMet ta yi hasashen cewa za a samu yanayin kura da hazo a wasu sassan ƙasar, yayin da wasu sassan za su fuskanci ruwan sama da iska.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com