Dakaru Sun Bazama Farautar Dogo Gide da Fitanannun Yan Bindiga 3 a Zamfara
- Dakarun OperationFansar Yamma sun fara kari hari tare da neman fitinannun 'yan ta'adda da su ka addabi mazauna jihar Zamfara da kewaye
- Harin sama da na ƙasa sun tarwatsa yunkurin taruwar ɗaruruwan ‘yan ta’adda tare da kashe da dama daga cikinsu a lokacin da su ke tattaunawa
- Sojojin sun samu nasarar kwato harsasai yayin da dakaru ke ci gaba da sintiri domin hana ‘yan ta’adda sake samun mafaka a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma (OPFY), sun ƙaddamar da wani gagarumin farmaki a jihar Zamfara.
An kai farmakin da nufin tarwatsa fitattun shugabannin ‘yan ta’adda huɗu, wato Dogo Gide, Najaja, Nasanda da Buba Oris, a wani samame da aka gudanar a Jihar Zamfara.

Source: Twitter
Rahotanni daga majiyoyin soja sun tabbatar wa Zagazola Makama cewa an fara aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 25 ga Yuli, 2026 kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
Sojoji sun kai hari Zamfara
Rahotannin sun kara da cewa ɗaruruwan ‘yan ta’adda masu ɗauke da makamai sun taru a bakin kogin Bayarzaki da ke Ƙaramar Hukumar Anka ƙarƙashin jagorancin waɗannan shugabanni huɗu.
A cewar majiyoyin, ana zargin ‘yan ta’addan suna shirin ƙaddamar da hare-hare a sassa daban-daban na Zamfara da ma jihohin da ke maƙwabtaka da ita kafin jami’an tsaro suka samu bayanan.
Bayan haka ne dakarun Operation Fansan Yamma suka kai hare-haren sama kan wuraren da aka gano ‘yan ta’addan a Barayan Zaki da kuma muhimman hanyoyin ketare kogin Bayarzaki.
Sojoji sun yi wa yan ta'adda kwanton bauna
A lokaci guda kuma, Dakarun Strike Force na runduna ta 8 suka kafa kwanton bauna a wurare masu muhimmanci kafin su ƙaddamar da farmakin ƙasa da sanyin safiya domin tare hanyar tserewar ‘yan ta’addan.
Majiyoyin soja sun ce haɗin gwiwar hare-haren sama da na ƙasa ya tarwatsa shirin ‘yan ta’addan, lamarin da ya tilasta masu barin sansanoninsu tare da yunƙurin tserewa ta Barayan Zaki domin ketare Babbar Hanyar Gummi–Anka.

Source: Original
Dakarun sun ci gaba da sintirin yaƙi a hanyoyin da ake zargin sun bi wajen tserewa. Wannan ya kai ga wani mummunan artabu a Kombo da ke kan hanyar Anka–Gummi a Ƙaramar Hukumar Bukkuyum.
A yayin artabun, sojojin sun yi amfani da ƙarfin wuta mai yawa wanda ya yi sanadin kashe da dama daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da sauran suka tsere cikin ruɗani zuwa dazukan da ke kusa.
Matawalle ya ba sojoji umarni
A baya, mun kawo labarin cewa karamin Ministan Tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba dakarun Operation Fansan Yamma da sauran rundunonin soji da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma Sabon umarni.
Matawalle ya bayar da umarnin ne yayin da yake jajanta wa waɗanda hare-haren 'yan ta'adda na baya-bayan nan suka shafa a Bungudu da sauran al'ummomin Zamfara da ke fama da rashin tsaro.
Ministan ya umarci sojoji da su ƙara sanya ido da sintiri domin gano maboyar 'yan ta'adda tare da lalata su kafin su sake amfani da su wajen kai hare-hare a kan bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba.
Asali: Legit.ng

