Muƙamin Minista: Pantami Ya Samu Kariya, an Ƙalubalanci Tsohon Jami'in DSS

Muƙamin Minista: Pantami Ya Samu Kariya, an Ƙalubalanci Tsohon Jami'in DSS

  • Na kusa da tsohon minista, Farfesa Sulaiman Muhammad ya kare Isa Ali Pantami kan nada shi mukamin minista a Najeriya
  • Ya ce Pantami ya kalubalanci Mohammed Yusuf tun 2006, sannan Shekau ya yi masa barazanar kisa bayan aiwatar da tsarin NIN-SIM
  • Farfesan ya ce ya dace a auna Pantami da tarihin aikinsa, musamman gudummawar da ya bayar wajen inganta tsaron Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Makusancin tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya ƙare malamin kan nada shi mukami.

Farfesa Sulaiman Muhammad ya kare Pantami, kan muhawarar da ta sake tasowa bayan tsohon jami'in DSS, Dennis Amachree ya wallafa tarihin rayuwarsa.

An kare Pantami kan sukar nadin da Buhari ya yi masa
Tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami da marigayi Muhammadu Buhari. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Farfesan ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya yi wanda Legit Hausa ta samu kan sukar tsohon ministan sadarwa, Isa Pantami.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya sake magana kan sulhu da ƴan bindiga, ya yaba Jonathan, Osinbajo

Mukamin Pantami: Shawarar da aka ba jama'a

Sulaiman ce ya kamata a yi hukunci kan lamarin bisa hujjoji, cikakken tarihi da bayanan da aka tabbatar, ba tare da cire abubuwa daga mahallinsu ba.

Ya bayyana cewa cece-kucen da suka taso a shekarar 2021 sun samo asali ne daga tsofaffin hudubobin addini da Pantami ya gabatar tsakanin shekarun 2001 da 2002.

A cewarsa, Pantami ya bayyana cewa kalaman nasa sun fito ne lokacin da yake cikin fushi saboda kashe-kashen bayin Allah da gazawar tsarin tsaro wajen kare rayuka.

Sulaiman ya ce Pantami ya jaddada sau da dama cewa bai taba goyon bayan kashe bayin Allah ba bisa doka ba, kuma fassara kalamansa a matsayin goyon bayan ta'addanci ba ta dace ba.

Ya kuma tunasar da cewa a watan Yunin 2006 Pantami ya yi muhawara ta tsawon sa'o'i shida da wanda ya kafa Boko Haram, Mohammed Yusuf, inda ya kalubalanci akidarsa kan ilimin zamani.

An caccaki masu sukar ba Pantami mukami
Tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami da marigayi Muhammadu Buhari. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Yadda fahimtar Pantami ta sauya kan lamura

Kara karanta wannan

Tsaro: Tsohon daraktan DSS ta dura kan Pantami, ya faɗi illar naɗa shi minista

Farfesan ya ce lokacin da tsofaffin kalaman suka sake bayyana a watan Afrilun 2021, Pantami bai guje wa tambayoyin jama'a ba, sai dai ya yi karin haske a darussan Ramadan da yake gabatarwa a Abuja.

Ya ce Isa Ali Pantami ya bayyana cewa fahimtarsa kan al'amuran duniya ta sauya saboda karin ilimi da gogewa, sannan ya yi watsi da duk wata akidar tsattsauran ra'ayi mai amfani da tashin hankali.

Har ila yau, ya kuma bukaci a duba tarihin aikin Pantami, yana mai cewa ya jagoranci aiwatar da tsarin hade lambar NIN da layin SIM domin dakile amfani da layukan da ba su yi rajista ba.

A cewarsa, wannan tsari ya taimaka wa jami'an tsaro wajen gano hanyoyin sadarwar masu garkuwa da mutane, 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya.

Ya kara da cewa shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi wa Pantami barazanar kisa a wani bidiyo da ya fitar a shekarar 2020 saboda matakan da suka takaita hanyoyin sadarwar kungiyar.

Sulaiman ya kammala da cewa ya dace a yi wa Pantami adalci ta hanyar auna shi da cikakken tarihin aikinsa, yana mai cewa gudummawar da ya bayar ga tsaron kasa da ci gaban tsarin yanar gizo na zamani ta cancanci yabo.

Kara karanta wannan

Shugaban kasar Bangladesh ya yi murabus kafin karewar wa'adinsa

Pantami ya fito da karfi kan takarar gwamna

A wani labarin, an ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana dalilinsa na shiga takarar gwamnan Gombe a 2027, yana mai korafi kan lalacewar lamura.

Pantami ya bayyana cewa babu wata al'umma da ta gyaru da kanta, yana mai cewa sai mutane sun tashi tsaye domin neman sauyi.

Tsohon ministan ya bukaci a shirya muhawara tsakanin dukkan 'yan takara, tare da binciken ayyukansu da ba da damar tonon silili kafin zaben gwamna na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.