Trump Ya Yi Maganganu da aka 'Gano' Makaman Amurka na Neman Karewa

Trump Ya Yi Maganganu da aka 'Gano' Makaman Amurka na Neman Karewa

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta rahotannin da ke cewa hare-haren da ƙasarsa ke kai wa Iran sun rage mata yawan makamai
  • Trump ya ce Amurka na da makamai fiye da kowace ƙasa a duniya, kuma fiye da abin da take buƙata domin kare muradunta
  • Kalaman shugaban na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun ce ana sa ido kan raguwar wasu manyan makamai da ake amfani da su a yaƙin Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington D.C. – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa hare-haren da ƙasarsa ke kai wa Iran sun fara rage yawan makaman da Amurka ke da su.

Hakan na zuwa ne bayan Trump ta dakatar da kai hare-hare kasar Iran ba tare da cimma manufar fara yakin ba, lamarin da yasa ake cewa da walakin wai goro a mita.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara fuskantar matsalar makamai, Trump ya dakatar da hare hare kan Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump na wani jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Maganar da Trump ya yi

Al Jazeera ta rahoto cewa Trump ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da 'yan jarida , inda ya ce Amurka na da makamai fiye da kowace ƙasa a duniya.

Trump ya ce:

"Muna da makamai fiye da kowace ƙasa a duniya, kuma fiye da abin da muke buƙata."

Ya yi wannan bayani ne domin mayar da martani ga rahotannin da Wall Street Journal da CNN suka wallafa, waɗanda suka nuna cewa ci gaba da kai hare-hare da kuma kare sansanonin Amurka ya ƙara rage yawan wasu muhimman makamai.

Rahotannin sun ce jami'an soja na bibiyar adadin makamai irin su Patriot, Tomahawk da kuma SM-3, waɗanda aka yi amfani da su sosai wajen dakile makamai masu linzami da jiragen yaƙin marasa matuƙa na Iran.

Ya ake ciki a Gabas ta Tsakiya?

Rahotannin sun kuma nuna cewa an shafe dare biyu a jere ba tare da Amurka ta kai sabon hari kan Iran ba, yayin da Tehran ita ma ta dakatar da hare-haren ramuwar gayya a yankin.

Kara karanta wannan

An yada bidiyon Trump ya dungura kasa yayin shiga mota, shin da gaske ne?

Haka kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce an samu ci gaba a tattaunawar da ake yi da Oman kan yadda za a tafiyar da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump a fadar White House. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya zargi Ukraine da kai hari kan wani jirgin kasuwancin Iran a tekun Caspian, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani ma'aikacin jirgin.

Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun kuma bayyana cewa wani jirgin dakon mai ya fashe bayan ya taka nakiyar ruwa a mashigar Hormuz.

Bidiyon Trump ya bazu a intanet

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin nuna Donald Trump yana faɗuwa yayin shiga motarsa ta shugaban ƙasa.

Sai dai bincike ya tabbatar da cewa bidiyon ba na gaskiya ba ne, domin an ƙirƙire shi ne ta amfani da fasahar AI, ba tare da Trump ya faɗi a zahiri ba.

Duk da haka, wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun gaskata bidiyon, inda suka nuna damuwa kan lafiyar shugaban Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng