'Yan APC Sun Tayar da Hayaniya a Legas, An Yi Zanga Zanga kan Zaɓen Fitar da Gwani
- Magoya bayan jam'yya mai mulki ta APC sun gudanar da zanga-zanga kan sakamakon zaben fitar da gwani a Agege da ke jihar Legas
- Masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa an sauya sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓen, lamarin da suka ce ya saba da dokar jam'iyya
- Shugaban APC na jihar Legas ya bukaci masu korafi da su bi hanyoyin da suke da su a cikin jam'iyya wajen neman adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Jam’iyyar APC a jihar Legas ta shiga rudani bayan 'ya'yanta sun yi zanga-zanga a ranar Talata 9 ga watan Yuni, 2026.
Wannan ya biyo wasu daga cikin 'yan jam'iyyar sun nuna rashin amincewa da sakamakon zaben fitar da gwani na kujerun majalisar dokokin jihar da aka gudanar a mazabun Agege I da Agege II.

Kara karanta wannan
Babu zancen shari'ar Musulunci: Ƴan bindiga da suka sace dalibai a Oyo sun fadi bukatunsu

Source: Twitter
Rahoton jaridar Punch ta wallafa cewa masu zanga-zangar sun mamaye sakatariyar APC da ke Ogba, suna dauke da alluna masu dauke da sakonni daban-daban da ke nuna adawarsu ga sakamakon da jam’iyyar ta fitar.
'Yan APC a Legas sun yi zanga-zanga
A ruwayar Daily Trust ta wallafa cewa 'yan APC sun yi zargin cewa sunayen da aka bayyana a matsayin wadanda suka yi nasara ba su dace da sakamakon kuri’un da aka kada ba.
Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar APC ta bayyana Abiola Oluwagbemiga a matsayin wanda ya lashe tikitin Agege I, yayin da Sule Akindele ya samu tikitin Agege II.
Sai dai masu zanga-zangar sun ce kuri’unsu sun bai wa Ganiyu Egunjobi nasara a Agege I, yayin da Azeez Yusuf, wanda aka fi sani da Ninalowo, ya yi nasara a Agege II.
A yayin zanga-zangar, sun rika rera wakoki da daga alluna masu dauke da sakonni kamar:

Kara karanta wannan
Tsofaffin shugabannin majalisa da suka yi murabus daga APC kan zaben fitar da gwani
"Hamzat, kada ka lalata dimokuradiyyarmu," da kuma "Ku bari muradin jama’a ya yi nasara."
Kiran APC ga masu zanga-zanga
A nasa bangaren, shugaban APC na jihar Legas, Cornelius Ojelabi, ya bukaci duk wadanda ke da korafi su bi hanyoyin da jam’iyyar ta tanada domin warware matsaloli.

Source: Twitter
Ta cikin sanarwar da Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Omobola Akingbehin, ya fitar jam’iyyar ta bayyana cewa an kammala aikin zaben fitar da gwani, kuma akwai tsare-tsaren cikin gida da aka kafa domin sauraron korafe-korafe.
Sanarwar ta ce jam’iyyar na mutunta hakkin kowa na bayyana damuwarsa ta hanyar doka, amma dole ne a yi hakan cikin lumana tare da kiyaye dokokin jam’iyya da zaman lafiya.
Mutanen Atiku sun koma APC
A baya, mun wallafa cewa wata ƙungiyar wayar da kan matasa da ke da alaƙa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ta sanar da cewa ta koma APC mai mulki.
Kungiyar ta bayyana cewa tana goyon bayan sake zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027, tare da alƙawarin samar masa da ƙuri’u miliyan 10 daga 'yan Najeriya da za su yi zabe.
Ta bayyana hakan ne a wajen bikin ƙaddamar da ita wanda kuma a nan ta fadi tsarinta na wayar da kan jama’a tare tabbatar da haɗuwarta da City Boy yayin da ake shirin tunakarar zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng