Tsaro: Gwamna Ya Ce ko za a Sace Kowa a Najeriya Tinubu zai Zarce a 2027

Tsaro: Gwamna Ya Ce ko za a Sace Kowa a Najeriya Tinubu zai Zarce a 2027

  • Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya zargi jam’iyyun adawa da amfani da matsalar rashin tsaro domin bata sunan gwamnatin shugaba Bola Tinubu
  • Okpebholo ya yi wannan magana ne a ranar Talata yayin kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar APC na zabukan kananan hukumomi a Edo ta Kudu
  • Gwamnan ya ce yada rashin tsaro ba zai ba jam’iyyun adawa damar samun kujerun majalisar dattawa, majalisar wakilai ko shugabancin kasa ba a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya yi zargin cewa wasu mutane na karawa rashin tsaro karfi domin karkatar da hankalin shugaba Bola Tinubu.

Ya fadi haka ne da yake jawabi yayin kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar APC na zabukan kananan hukumomi a zaben da za a yi a Edo.

Kara karanta wannan

Sabon kudiri: Ana son shugaban kasa ya dawo yin shekara 6 ba tazarce a Najeriya

Monday Okpebholo da wasu 'yan APC
Gwamna Monday Okpebholo na magana a wajen taron APC a Edo. Hoto: @m_akpakomiza
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan ya ce rashin tsaro ya karu kwatsam a kasar nan, yana mai zargin cewa ana shirya hakan ne domin bata shugabancin shugaba Bola Tinubu.

Maganar zaben 2027 da rashin tsaro

Gwamna Okpebholo ya ce kara matsalar rashin tsaro ba za ta ba masu aikata hakan damar samun kujerun majalisar dattawa, majalisar wakilai ko shugabancin kasa ba, domin babu mai iya korar Tinubu Aso Rock.

“Babu mai shiga Aso Rock. Ko da za su sace mu gaba daya, ba za su samu damar shiga Aso Rock ba.”
“Sun gaza. Ba su gaza ba ne? Ta hanyar yin garkuwa da yara? To wa za ku mulka? Ba za a samu wanda za ku mulka ba. Don haka su bari a zauna lafiya domin mu yi mulki yadda ya kamata,”

In ji Okpebholo.

Ayyukan da Bola Tinubu ya yi

Gwamnan Edo ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wa Najeriya aiki fiye da wadanda suka gabace shi a shekarun da suka wuce.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta kashe Naira biliyan 10, Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa a yaki Ebola

Premium Times ta wallafa cewa ya ce an ga amfanin cire tallafin man fetur a ayyuka daban-daban da ke gudana a fadin jihar Edo da kewaye.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na yi wa jama'a bayani a taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Maganar Okpebholo kan zaben APC

Okpebholo ya yaba wa wadanda suka yi nasara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar domin zama ‘yan takara a zabukan kananan hukumomi masu zuwa.

Ya ce nasararsu za ta nuna yiwuwar cika alkawarin kuri’u miliyan 2.5 da aka yi wa shugaba Tinubu a babban zaben shekarar 2027 a jihar.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban jam’iyya a jihar, Jarrett Tenebe, ya bayyana APC a matsayin jam’iyya daya tilo mai karfi a Edo.

Ya bukaci ‘yan takarar su rika fadin ayyukan ci gaban da gwamnan ke yi a kowane lungu da sako na jihar, tare da kwaikwayon irin wadannan ayyuka a kananan hukumominsu.

Ali Ndume ya gargadi Gwamnatin Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya yi gargadin cewa babban zaben shekarar 2027 zai kasance fafatawar siyasa mai zafi ga Bola Tinubu.

'Dan majalisar ya ce duk da cewa jam’iyyar APC babbar jam’iyya ce mai karfi, zai kasance rashin dabara a raina masu kalubalantar ta.

Kalaman nasa sun biyo bayan rade-radin cewa manyan 'yan adawa, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi da Gwamna Seyi Makinde, na iya kulla kawance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng