Fitaccen Mai Barkwanci a Najeriya, AY Ya Daina zuwa Coci, Ya Fadi abin da Ya Faru

Fitaccen Mai Barkwanci a Najeriya, AY Ya Daina zuwa Coci, Ya Fadi abin da Ya Faru

  • AY Commedian ya ce ya daina zuwa coci na wani lokaci saboda rade-radin da ake yi kansa bayan ya shiga wata matsala ta rayuwa
  • Fitaccen mai barkwancin dan Kudancin Najeriya ya ce wata coci ta janye gayyatarsa zuwa wani shiri saboda yadda jama'a ke kallonsa
  • A cewar Ayo Makun, ya kamata coci ta kasance wurin gafara, gaskiya da dawo da jawo neman taimako ga ubangiji a jiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Abuja – Fitaccen ɗan wasan barkwanci kuma jarumin fim a Najeriya, Ayo Makun (AY), ya bayyana dalilin da ya sa ya daina halartar ibadar coci na wani lokaci.

A cewar 'AY Commedian,' ya janye daga zuwa coci ne biyo bayan mummunar fahimtar da mutane suka yi game da shi a kafafen sada zumunta.

AY ya bayyana dalilinsa na daina zuwa coci na wani lokaci
Fitaccen dan wasan barkwanci a Najeriya, AY da ya daina zuwa coci na wani lokaci. Hoto: @comedianay
Source: Instagram

Dalilin AY na daina zuwa coci

Kara karanta wannan

Matar aure ta kwarawa kishiyarta mai ciki ruwan zafi, ta haihu dan ya mutu

AY ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Lahadi, inda ya ce bai daina zuwa coci ba saboda ya rasa bangaskiyarsa ga ubangiji.

Sai dai ya daina zuwa coci ne saboda yana cikin wani mawuyacin hali na rayuwa kuma ba ya son ya zama abin rade-radi tsakanin masu ibada, a cewarsa.

Ya ce bayan labarai da rubuce-rubucen da suka yadu game da shi a shafukan yanar gizo, ya ga dacewar ya ja baya na wani lokaci domin kauce wa kallon da mutane za su rika yi masa da kuma maganganun sirri a cikin coci.

"Na daina zuwa coci na wani lokaci ba don na daina gaskata Allah ba, kuma ba don bangaskiyata ta gushe ba. Ina cikin wani mawuyacin hali ne, sannan aka baza wasu labarai marasa dadi a kaina. Na zabi na ja baya ne saboda ba na son in zama abin rade-radi a gidan Allah," in ji shi.

Yadda aka janye gayyatar AY a coci

Dan wasan barkwanci AY ya ce duk da cewa yana bin wasu ibadu ta intanet, daga baya ya samu karfin guiwar komawa wata coci, inda fasto, iyalansa da shugabannin cocin suka tarbe shi cikin mutunci.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da turawa 11 ya yi hatsari a Amurka, ya kamata da wuta

Sai dai ya ce bayan an gayyace shi domin shiga wani shirin coci, daga bisani an sanar da shi cewa an janye gayyatar bayan wasu tattaunawa a cikin shugabancin cocin saboda yadda jama'a ke kallonsa.

AY ya ce ya mutunta matakin da aka dauka, amma hakan ya sa ya fara tambayar kansa ko ra'ayin jama'a ya fi muhimmanci fiye da alakar mutum da Allah.

Ya ce ba ya kokarin suka ga fastoci ko kare kansa daga zarge-zargen da ake yadawa a kansa, sai dai abin da ya faru ya sa ya yi tunani kan hakikanin manufar coci.

"Ya kamata coci ta zama mafakar masu neman gafara"

AY ya ce ko da duk abin da ake fada game da shi gaskiya ne ko karya ce, coci ya kamata ta kasance wurin da mutum zai samu gaskiya, gafara da damar gyara rayuwarsa.

AY ya ce ya kamata coci ta zama mafakar masu neman gafara
Fitaccen dan wasan barkwanci a Najeriya, AY da ya daina zuwa coci na wani lokaci. Hoto: @comedianay
Source: Instagram

Ya jaddada cewa Yesu Almasihu ya gayyaci duk masu nauyin damuwa da su zo gare shi ba tare da la'akari da abin da mutane ke fada a kansu ba.

Jarumin ya kuma yi ishara da ayoyin Littafi Mai Tsarki da ke nuna cewa kowa mai zunubi ne, yana mai tambayar Kiristoci da mabiyansa cewa:

Kara karanta wannan

Ndume ya musanta zargin shiga tsakani da 'yan bindiga, ya nemi a binciki Kaigama

"Idan mutane ba za su iya gudu zuwa gidan Allah ba lokacin da rayuwa ta yi musu nauyi, to ina ya kamata su je?"

AY ya kammala da tambayar da ya ce tana bukatar kowa ya yi tunani a kanta: "A hakikanin gaskiya, don su wa aka samar da coci?"

Kalli bidiyon a kasa:

Dan wasan barkwanci ya rasu

A wani labari, mun ruwaito cewa, fitaccen ɗan wasan barkwanci, Sanku, ya rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Oyo–Ogbomoso.

Kafin rasuwarsa, ya wallafa bidiyo a shafukansa na sada zumunta, yana addu’a kada ya mutu kafin ya ci gajiyar sana'ar barkwancinsa.

A tare da Sanku, akwai wasu abokansa da haɗarin ya rutsa da su, inda aka ji halin da suke ciki bayan da aka sanar da rasuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com