Latest
Davido ya ce ba zai nemi afuwar Gwamnan Edo, Monday Okpebholo ba, kan wallafa sakamakon WAEC da ake zargin na gwamnan ne wanda ya jawo cece-kuce.
Mawaki Davido ya ce zai iya yin caca da kuɗinsa kan sake zaɓen Tinubu a 2027, yana mai cewa rarrabuwar ‘yan adawa na ƙara wa shugaban ƙasa damar nasara.
Jaruma Doris Ogala ta bayyana aniyarta ta neman kujerar gwamnan jihar Abia a 2027, tana mai cewa kiran Allah ne ya sa ta shiga takarar domin kawo sauyi.
Kungiyar G100 ta gana da yan adawa ta Majalisar Wakilai domin haɗa kan ‘yan adawa da ƙalubalantar Bola Ahmed Tinubu da APC a zaɓen shekarar 2027.
Atiku Abubakar ya bayyana yadda ya ƙi Bola Tinubu a matsayin mataimakinsa saboda adawarsa da tikitin Musulmi da Musulmi, tare da bayyana sharudɗan hadewa da Buhari.
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya fito fili ya musanta jita-jitar cewa ya ƙulla yarjejeniyar siyasa da ADC domin murƙushe jam’iyyar APC a zaɓen da aka kammala.
Kungiyoyin manyan makarantun gwamnatin Gombe sun ba gwamna Inuwa Yahaya kwana 14 ya warware matsalolinsu ko su dauki mataki ciki har da shiga yajin aiki.
Peter Obi ya bukaci ‘yan siyasa su gudanar da yakin neman zaben 2027 cikin zaman lafiya, tare da tabbatar da cewa babu dan Najeriya da zai mutu saboda zabe.
Ministan birnin Abuja, Nyesom Wike ya ce da Bola Tinubu ya so APC ta lashe Osun, da ya taimaka masa, sannan ya ce zaɓen 2027 zai fi sauƙi ga shugaban ƙasa.
Masu zafi
Samu kari