Ibtila'i Ya Aukawa Masu Hakar Ma'adanai a Bauchi, an Rasa Rayuka

Ibtila'i Ya Aukawa Masu Hakar Ma'adanai a Bauchi, an Rasa Rayuka

  • Masu hakar ma’adinai tara sun mutu bayan ruwa ya mamaye ramin hakar ma’adanai sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a Bauchi
  • ’Yan sanda sun ce an ceto wasu daga cikin ma’aikatan, amma daga bisani aka fitar da sauran takwas daga ramin, inda aka tabbatar da mutuwarsu
  • Marigayin sun fito daga Bauchi, Nasarawa, Kogi da Kebbi, yayin da ’yan sanda suka ce ana ci gaba da bincike kan musabbabin faruwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Akalla masu hakar ma’adanai tara sun mutu bayan ambaliyar ruwa ta mamaye wani ramin da suke hakar ma’adanai a Bauchi.

Lamarin ya auku ne a ƙauyen Nahuta, Gundumar Gwana, ƙaramar hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.

Masu hakar ma'adanai sun mutu a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Bauchi, SP Nafiu Habib, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da Daily Trust ranar Laraba, 30 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tattara manoma kusan 50 zuwa daji, sun nemi makudan kudin fansa

Ruwan sama ya cika ramin da ruwa

Habib ya ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 27 ga Satumba, lokacin da ma’aikatan ke aikin hakar ma’adanai a wani rami da ya cika da ruwa sakamakon ruwan sama mai ƙarfi.

A cewarsa, Kasim Abdulsalam, manajan da ke kula da sayayya na kamfanin Zurfi Mining Company da ke Nahuta, ne ya kai rahoton lamarin ga ’yan sanda.

Ya ce ma’aikatan ’yan kwangila ne da ke aiki a Ramin Haka na Uku, inda ruwa ya mamaye wurin bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi da misalin ƙarfe 3:00 na rana ranar 25 ga Satumba.

An yi ƙoƙarin ceto ma’aikatan

Kakakin ’yan sandan ya ce an yi nasarar ceto wasu daga cikin ma’aikatan, yayin da wani daga cikinsu ya gamu da ajalinsa bayan wutar lantarki ta taba shi.

An garzaya da shi zuwa Babban Asibitin Kashere, da ke ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke matasa saboda sanya rigar 'Tinubu Must Go'

Habib ya ce DPO na Alkaleri ya jagoranci jami’an bincike zuwa wurin, inda suka tarar da injinan famfo guda uku suna fitar da ruwa daga cikin ramin domin ba da damar ceto sauran ma’aikatan.

An fitar da sauran gawarwaki takwas

Ya ce daga bisani an fitar da sauran ma’aikata takwas daga ramin da misalin ƙarfe 6:20 na safiyar 28 ga Satumba.

An kai su asibitin da aka kai mutumin da ya mutu a baya, inda likita ya tabbatar da cewa dukkaninsu sun rasu.

Mutanen da suka mutu sun haɗa da Hamidu Ali, mai shekaru 40, Saidu Abubakar, mai shekaru 29, da Olije Abdulrazak, mai shekaru 25, waɗanda suka fito daga jihohin Nasarawa da Kogi.

Sauran sun haɗa da Musa Abdullahi, mai shekaru 29, Abdulrahman Mu’azu, mai shekaru 23, da Jafar Abbas, mai shekaru 24, dukkansu daga Jihar Bauchi.

Sauran biyu su ne Jose Ukese, mai shekaru 28, daga Jihar Nasarawa, da Haruna Alkali, mai shekaru 30, daga Jihar Kebbi.

Masu hakar ma'adanai sun mutu a Bauchi
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kashe masu hakar ma'adanai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Akalla masu haƙar ma’adinai biyar aka harbe har lahira, yayin da wasu mutum biyu suka samu raunuka bayan ’yan bindiga sun kai hari a jihar Plateau.

Maharan sun rutsa mutanen ne a wurin haƙar ma’adinai da ke ƙauyen Marit, ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta jihar Plateau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng