Peter Obi Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya ba 'Yan Siyasa Shawara kan Zaben 2027

Peter Obi Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya ba 'Yan Siyasa Shawara kan Zaben 2027

  • Peter Obi ya bukaci ’yan siyasa su tabbatar da cewa babu dan Najeriya da ya rasa ransa saboda zabe a shekarar 2027
  • Dan takarar na NDC ya ce ya kamata ’yan takara su yi kamfen bisa batutuwan da suka shafi rayuwar ’yan Najeriya
  • Obi ya bukaci a gudanar da zabe inda kuri’un jama’a za su yi tasiri, yana mai cewa makomar ’yan Najeriya ta dogara da hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, ya bukaci masu ruwa da tsaki a siyasa su tabbatar da cewa babu dan Najeriya da ya rasa ransa saboda zabe.

Peter Obi ya kuma yi kira ga ’yan takara su gudanar da kamfen bisa batutuwa gabanin babban zaben 2027.

Peter Obi ya ba 'yan siyasa shawara kan zaben 2027
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya bayyana hakan ne ranar Talata, 18 ga watan Agustan 2026, yayin da ya isa wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa da Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa, tare da hadin gwiwar Cibiyar Kukah, suka shirya a Abuja, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

"Jama'a sun waye": Jigo a APC ya hango abin da zai sanya Tinubu ya fadi a 2027

Ya ce dole ne ’yan takarar da ke neman mukaman gwamnati su tabbatar da cewa halayensu da dabi’unsu sun dace da nauyin da ke tattare da mukaman da suke nema.

Peter Obi ya bukaci kamfen mai lumana

“Ina sa ran za mu samu kamfen cikin lumana, wanda zai mayar da hankali kan batutuwa. Domin kare martabar kasar nan, dole ne mu tabbatar da cewa halayenmu sun dace da mukamin da muke nema, dabi’unmu su dace, mu yi abin da ya dace sannan mu yi kamfen kan batutuwan da ’yan Najeriya ke fuskanta a yau.”

Da yake magana kan zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala, tsohon gwamnan jihar Anambra ya nuna bakin cikinsa kan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harkokin zaben.

Ya bukaci shugabannin siyasa da ’yan Najeriya kada su manta da wadanda suka mutu a lokacin zaben, yana mai kira da a tallafa wa iyalansu tare da jajanta musu.

Kara karanta wannan

Yadda motoci suka nutse, komai ya tsaya cak bayan ambaliya a Abuja

Obi ya nemi a bari kuri'u su yi tasiri

Dan takarar na NDC ya kuma yi kira da a samu tsarin zabe inda kuri’un jama’a za su yi tasiri na hakika, yana mai cewa hakan na da muhimmanci ga makomar ’yan Najeriya.

“Ba ni da wani tsoro sai dai in ce, don Allah, saboda ’yan Najeriya, za mu iya samun zaben da kuri’ar jama’a za ta yi tasiri?” In ji shi.

Da aka tambaye shi irin hukuncin da ya kamata a dauka kan jam’iyyu ko ’yan takarar da suka karya alkawuran da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiyar, Obi ya ce masu kada kuri’a su yi amfani da kuri’unsu wajen hukunta irin wadannan ’yan siyasa.

Da aka sake tambayarsa irin hukuncin da ya kamata a kakaba wa wadanda suka karya yarjejeniyar, Obi ya amsa da cewa:

“Hukuncin shi ne Najeriya kada ta zabe su. Amin.”
Peter Obi ya ba 'yan siyasa shawara
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Dalilin Kwankwaso na aiki tare da Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sanya ya amince ya zama abokin takarar Peter Obi.

Kwankwaso ya ce ya amince da zama abokin takarar Peter Obi a zaben 2027 ne saboda bukatar daidaiton kasa, adalci da kawo sauyin dimokuradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng