'Ba Mu ga Dama ba ne': Wike Ya Faɗi Abin da Za Su Yi da Tinubu Su Kwace Osun
- Nyesom Wike ya ce da Shugaba Bola Tinubu ya so APC ta lashe zaɓen Osun da ƙarfi, da ya taimaka masa, kuma Adeleke ba zai iya hana nasarar ba
- Wike ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta yi amfani da ƙarfinta wajen karkatar da zaɓen Osun ba, wanda Ademola Adeleke ya lashe
- Ministan ya yi hasashen cewa zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai fi sauƙi ga Tinubu saboda ya ce jam’iyyun adawa sun raunana sosai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Nyesom Wike, ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, ya yi maganganu kan zaben jihar Osun da aka gudanar.
Wike ya ce da Shugaba Bola Tinubu ya so APC ta lashe zaɓen gwamnan Osun da ƙarfi, da ya taimaka masa.

Source: Facebook
Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da yake duba wasu wuraren da ambaliyar ruwa ke yawan shafa a Maitama, Abuja, cewar TheCable.
Yadda Tinubu ya bar Accord ta ci zabe
Wike, wanda har yanzu mamba ne a jam’iyyar PDP, ya ce Tinubu da gangan ya bar zaɓen ba tare da tsoma bakin gwamnatin tarayya ba.
Ya ce da shugaban ƙasar ya zaɓi amfani da tasirinsa na siyasa wajen tabbatar da nasarar APC, da shi ma zai goyi bayan hakan, cewar Punch.
Wike ya ce:
“Da shugaban ƙasa ya so lashe zaɓen jihar Osun ko ta halin ƙaƙa, da na kasance a wurin, kuma da mun lashe shi, babu abin da gwamna zai iya yi."
An bayyana Ademola Adeleke, gwamnan da ke kan mulki kuma ɗan takarar Accord, a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 15 ga Agusta, bayan ya samu nasara a ƙananan hukumomi 19 cikin 30.
Bola Oyebamiji, ɗan takarar APC, ya samu nasara a sauran ƙananan hukumomi 11 da suka rage.
Wike ya ce sakamakon zaɓen ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ba ta yi amfani da tasirinta wajen karkatar da zaɓen domin APC ba.

Kara karanta wannan
Abin da ADC ta yi da ya taimaka wajen kayar da jam'iyyar APC a zaben gwamnan Osun
“Ba a yi amfani da ƙarfin gwamnatin tarayya a Osun ba. Idan ka ga ƙarfi da tasirin gwamnatin tarayya, za ka sani."
- In ji Wike.

Source: UGC
Yiwuwar komawar Adeleke APC
Ministan Abuja ya kuma nuna cewa da abubuwa sun kasance yadda ya kamata a cikin APC, da Adeleke zai iya kasancewa cikin jam’iyyar.
Wike, wanda ke ci gaba da goyon bayan Tinubu duk da kasancewarsa mamba a PDP mai adawa, ya kuma yi hasashen cewa zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai fi na 2023 sauƙi ga Tinubu.
Tsohon gwamnan Rivers ya danganta hasashensa da abin da ya bayyana a matsayin raunin jam’iyyun adawa.
Ya kara da cewa:
“Zaɓen 2027 zai kasance mafi sauƙi ga shugaban ƙasa idan aka kwatanta da na 2023, a wannan karon, an raunana adawa, ba ta da matsuguni, ba ta da wani ƙarfi."
Wike ya ci gaba da nuna goyon bayansa ga gwamnatin Tinubu duk da cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP mai adawa.
Wike ya gano yadda Tinubu zai lashe zaɓe
An ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda zaben Shugaba Bola Tinubu zai kasance a shekarar 2027.
Wike ya ce rarrabuwar kawunan jam’iyyun adawa da yawan sauya sheka sun raunana su, don haka ba za su iya kalubalantar Tinubu yadda ya kamata ba.
Ministan ya kuma umarci hukumomin Abuja su rusa gidajen da aka gina kan hanyoyin ruwa, yana mai cewa gwamnati na da cikakken ikon siyasa.
Asali: Legit.ng

