Magana Ta Fito: Yadda Addinin Tinubu Ya Hana Shi Zama Abokin Takarar Atiku a Zaben 2007
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya tuna dalilin da ya sa ya ƙi zaɓar Bola Ahmed Tinubu a matsayin mataimakinsa a 2007
- Atiku, wanda ke neman zama shugaban kasa karkashin inuwar ADC a 2027, ya ce ya ɗauki matakin ne domin kare muradun Najeriya
- Ya kuma bayyana yadda daga baya ya goyi bayan Muhammadu Buhari bisa sharadin cewa ba za a yi tikitin Musulmi da Musulmi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana yadda ya ƙi amincewa da wani yunƙuri na hada tikitin musulmi da musulumi tun a zaben 2007.
Atiku Abubakar ya ce ya yi fatali da bukatar gwamnan jihar Legas a wancan lokaci, Bola Ahmed Tinubu, na zama mataimakinsa, yana mai cewa ya yi adawa da tikitin Musulmi da Musulmi ne domin kare muradun ƙasa.

Kara karanta wannan
Cutar Apollo ta ɓarke a wasu jihohin Arewacin Najeriya, ta fara yaɗuwa cikin jama'a

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa a wata hira da aka yi da shi, Atiku ya bayyana yadda wasu dattawa suka je wurinsa bayan ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa, domin tattauna batun Tinubu na son zama mataimakinsa.
Yadda Atiku ya ƙi bukatar Tinubu
A cewarsa, Tinubu ya tura dattawa biyar, ciki har da Tom Ikimi, Bisi Akande da wasu mutum uku, domin su tattauna batun da shi.
“Ya ce zai mara min baya wajen samun tikitin. Bayan na samu tikitin, sai ya turo dattawa biyar cikinsu akwai Tom Ikimi, Bisi Akande da wasu mutum uku. Suka gaya min cewa Tinubu yana son ya zama mataimakina.
“Na gaya musu cewa, a matsayinsu na Kiristoci, ya kamata su fahimci cewa bai dace in zaɓi Musulmi ya zama mataimakina ba.
“Na tambaye su dalilin da ya sa ba za su iya gaya masa hakan ba. Na gaya musu cewa ba zan iya amincewa da tikitin Musulmi da Musulmi ba, saboda hakan ba zai kasance cikin muradun ƙasarmu ba.”
- Atiku Abubakar
Atiku da Tinubu sun rabu kafin zabe
Atiku ya ce daga baya Tinubu ya rabu da shi tare da mara wa marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua baya.
Ya ce daga wannan lokaci suka rabu, kuma ba su sake kasancewa a sansanin siyasa guda ba har zuwa shekarar 2014, lokacin kamfen ɗin Buhari.
Ya ce:
“Na koma Abuja bayan babban taron jam’iyya, sai marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarce ni a gidana.
“Ya gaya min cewa ya tsaya takara a zaben fidda gwani kuma ya yi nasara, amma yana buƙatar goyon baya domin ya ci babban zaɓen, yana cewa ba zai iya yin nasara ba tare da goyon bayana ba.”

Source: Facebook
Atiku ya gindaya sharadi ga Buhari
Atiku ya ce ya amince ya goyi bayan Buhari ne bisa wani sharadi, saboda ya ji cewa Tinubu na son Buhari ya zaɓe shi a matsayin mataimakinsa.
Ya ce ya tabbatar wa Buhari cewa zai mara masa baya idan har ba zai yi tikitin Musulmi da Musulmi ba, cewar rahoton Vangaurd.
“Na ba shi sharadi guda saboda na ji cewa Tinubu yana son Buhari ya zaɓe shi a matsayin mataimakinsa. Na tabbatar masa cewa zan goyi bayansa bisa sharadin cewa ba zai yi tikitin Musulmi da Musulmi ba.
“Bayan ya yi tunani na kusan mintuna biyar, ya tabbatar min cewa ba zai yi hakan ba,” in ji Atiku.
Atiku ya sake sukar gwamnatin Tinubu
Kun ji cewa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da dora wa gwamnatocin baya alhakin matsalar matatun man fetur na Najeriya duk da shi ne a mulki.
'Dan takarar shugaban kasa a ADC ya ce gwamnatin yanzu ta kamata ta yi bayani kan makudan kudin da aka kashe wajen gyaran matatun
Asali: Legit.ng

